Daga: Ibrahim Sani Gama
Hukumar NAFDAC reshen jihar Kano ta cafke mutane shida tare da rufe wasu shaguna a kasuwar Sabon Gari, sakamakon kama da su da laifin sayar da man gyaran fata da ba shi da sahalewar hukuma.
Shugaban hukumar a jihar, Kasim Ibrahim, ya bayyana wa manema labarai a ranar Talata cewa matakin ya biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka shigar ta kafafen sada zumunta, wanda hakan ya janyo umarnin bincike daga shugabar hukumar ta ƙasa.
“A sakamakon korafe-korafen da muka samu, sai muka fara bincike cikin sirri, har ma muka sayi wasu daga cikin kayayyakin da ake zargin don tabbatar da ingancinsu,” in ji Ibrahim.
Binciken ya gano mutane shida da ake zargin suna da hannu wajen rarrabawa da amfani da man ba bisa ƙa’ida ba.
Ibrahim ya ƙara da cewa mayukan da aka kama na kama da kayan kwalliya ne, amma suna ɗauke da sinadarai masu haɗari waɗanda NAFDAC ba ta amince da su ba.
Tare da haɗin guiwar sashen bincike da aiwatar da dokoki na NAFDAC, an kama waɗanda ake zargi, an rufe shagunansu, sannan an dauki samfurin man domin gwajin dakin bincike.
Bugu da ƙari, an kuma rufe wasu kamfanonin da ke kwaikwayon kayayyakin da aka riga aka yi wa rajista, ko kuma suka karya ka’idojin hukumar, har sai an kammala bincike.
Ibrahim ya bukaci jama’a da su kasance masu lura da kayayyakin da ake sayarwa, su kuma rika sanar da NAFDAC idan suka gano wani abu da ya saba wa doka.
