Daga: Abdullahi Bashir

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanar da kafa dokar ta-ɓaci ta awanni 48 a Ƙaramar Hukumar Jos North, bayan wani mummunan hari da ya auku a Angwan Rukuba.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin da ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa matakin na nufin dawo da doka da oda a yankin.

Ya kuma bai wa mazauna jihar tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Haka zalika, Mutfwang ya ce gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin jinyar waɗanda suka jikkata, tare da shirya jana’iza mai kyau ga waɗanda suka rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Dr. Nasiru Gawuna Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Alhaji Aminu Dantata 

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda yayi wa jam’iyyar…

Direbobin NURTW Tashar Malam Kato Sun Yi Jimamin Rasa Babban Jigo A Kano

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen tashar malam…

Kwamitin Lafiya Na Masarautar Karaye Ya Ziyarci Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Kwamitin lafiya na Masarautar Karaye karkashin jagorancin Matawallen…

KNHA, JIBAL Sun Horas Da ’Yan Jarida Kan Rahotannin Majalisa

Daga: Muhammad Adamu Abubakar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano (KNHA), RT. Hon.…