Daga: Jamila Suleiman Aliyu 

Gwamnatin Kano ta sha alwashin marawa matasa, masu bukata ta musamman, da yara wajen gina gobensu.

Kwamishinar mata, yara da masu bukata ta musamman Hajiya Amina Abdullahi Sani HOD ce ta bayyana hakan a yayin gagarumin bukin ranar mata da ya gudana a dakin taro na gidan Gwamnati wanda ta jagoranta tare da raba tallafin jari ga masu sana’o’i mabambanta da kuma baje kolin kayan sana’ar da aka koyarwa matasa.

Kwamishinar ta ce ba zatayi kasa a gwuiwa ba wajen zakulo wa mata hakkokinsu a duk inda suke don shine silar zuwan ta wannan kujera.

HOD ta kuma bayyana gwamnan Kano da jajirtacce a fannin daya shafi mata domin yana tsayawa tsayin daka a harkar matan duk da mai dakin gwamnan Sayyada mlMaryam Abba Kabiru tana cikin jerin matan da aka karrama da lambar yabo.

Haka zalika, Kwamishinar ta ce, ma’aikatarta zata waro matasa da zasu koyi sana’ar Gurasa a wurin wata kwararriya da aka karrama Malama Binta mai Gurasa don a samu yawaitar matasa a harkar gasa Gurasar don ci gaban jihar Kano baki daya.

Daga cikin matan da aka karrama sun hadar da uwa mai dakin tsohon shugaban kasa Hajiya Maryam Abacha da Hajiya Gaji Fatima Dantata da Hajiya Azumi Namadi Bebeji da sauran shahararrun mata a dai raba jari ga mata kimanin dari tara da tamanin da takwas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Tantance Masu Filaye A Rimin Zakara Tare Da Biyan Diyya- kwamishina Abduljabbar 

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Gwamnatin jihar Kano ta kammala Shirin ta na kawo…

Muhimmancin Tsaro Da Kare Dukiyoyin Al’umma – Kwamared Saminu

Daga: Dantala Uba Nuhu Kura Babban kwamitin cigaban tsaron al’ummar ‘Yan-Danko dake…

Gwamnonin Arewa Sun Fara Daukar Sabbin Matakai Don Tunkarar Ta’addanci

Daga: Sani Idris Maiwaya A kokarinsu na fuskantar matsalar tsaro da ta…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Haɗin Gwiwa Da Bankin Raya Musulunci Na Duniya Domin Ciyar Da Jihar Gaba

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo,…