Daga: Mukhtar Yahaya Shehu 

Gwamnatin jihar Kano ta kammala Shirin ta na kawo karshen rikicin kasa da ke faruwa tsakanin Jami’ar Bayero da ke nan kano da Kuma Al’umar yankin filin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo.

Kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ne ya sanar da haka yayin duba yadda aikin Tantance Masu Filaye da wadanda za a biya su Diyya da wasu filayen wasu Kuma a ba su kudade a harabar ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jiha.

Ya ce aikin Tantancewar da ya shiga rana ta biyar ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta samu nasarar Tantance kimanin mutane 500 da ke da filotai da Kuma gonaki, yayin da Kuma a hannu guda aka Fara Tantance Wadanda za a biya su Diyya ta kudi.

“Abin da na ke so in kira ga mutane cewa duk Wanda ya ke da fili a yankin Rimin Zakara ba a biya shi hakkin sa ba, to ya gaggauta zuwa ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jiha domin Mika koken sa domin ganin an share masa hawayensa.” In ji kwamishina Abduljabbar

Kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya kara da cewa aikin Tantancewar masu filayen na gidan na ne cikin tsari guda biyu wato bayan Tantance wa da ma’aikatar kasa ke yi Sai mutum ya ziyarci hukumar tsaro ta farin kaya domin Tantance bayanan sirri a kokarin tabbatar da sahihan wadanda ke da hakkin falayen domin ba su hakkin su.

“Gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na kokari domin tabbatar da adalci a tsakanin kowa ba tare da an cuce shi ba. Domin a baya mun fahimci ana Aringizo a sha’anin Tantancewar shi ya sa muka dakatar kafin daga bisani a halin yanzu mu cigaba da aikin Tantancewar.” A cewar kwamishinan.

Kwamishina Abduljabbar Muhammad Umar ya kara da cewa a cikin mutane sama da 200 da aka Tantance a ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jiha wadanda suka ziyar ci hukumar tsaro ta farin kaya domin Tantance su a mataki na biyu ba su fi mutane 70 ba. Inda ya ce lamarin akwai Lauje–cikin-nadi wato ko wasu basu da gaskiya ko Kuma ba ‘yan asalin yankin bane.

Ya ce wannan turka-turka ya faru ne tsawon Shekaru masu yawa da Suka shude wannan wuri mallakar Jami’ar Bayero ne, amma aka samu wasu masu son zuciya Suka yayyamka filotai suna sayar wa. Bisa haka ne ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jiha ta shiga cikin lamarin domin bai wa kowa hakkin sa.

“A halin yanzu gwamnatin jihar Kano ta na mallakawa duk Mai fili filinsa da Kuma Wadanda aka biya su Diyyar fili ko gine -ginensu sun yi gini a tsararren wuri da gwamnatin ta basu. In ji kwamishina Abduljabbar.

Malam Abubakar da Kuma Alhaji Aminu Hashim na daga cikin Al’umar yankin na Rimin Zakara da Suka halarci Tantancewar a ma’aikatar kasa sun Kuma nunan farin cikin su bisa shigar gwamnatin jihar Kano cikin lamarin domin kawo musu dauki ta hannun ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jiha.

Shi ma Shugaban masu dillancin filaye Awon gwamnati na jiha Alhaji Muhammad Kabir Ilyasu yaba wa gwamnatin jihar Kano ya yi ta hannun ma’aikatar kasa da tsare bisa yadda take kokari a sha’anin kawo karshen matsalar hada hadar filaye ba bisa ka’ida ba a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano Ta Shirya Gina Goben Masu Bukata Ta Musamman

Daga: Jamila Suleiman Aliyu  Gwamnatin Kano ta sha alwashin marawa matasa, masu bukata…

Taura Na Shirin Fuskantar Manyan Sauye-Sauyen Tattalin Arziki – Hambali

Daga: Kabir Getso  Shugaban Karamar Hukumar Taura, Hon. Dr. Shua’ibu Ibn Hambali, ya…

Jami’ar Al-hikma Ta Bada Gurbin Karatun Mutum Uku Kyauta Daga Iyalan Mamatan ‘Yan Wasan Kano

  Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22…

Makarantar Abdullahi Bn Mas’ud Da Ke Kuntau Ta Gudanar Da Bikin Saukar Alƙur’ani Karo Na Shida 

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Dalibai Maza Da Mata Dari Da Sittin Da Uku…