Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa 

Akalla mutane 750 ne suka ci gajiyar tallafin bada magani da duba marasa lafiya kyauta da Hon. Abdullahi Nasir Mai Kwano, mai neman takarar kujerar Majalisar Jiha a Karamar Hukumar Warawa karkashin jam’iyyar NDC, ya dauki nauyi.

Tallafin ya hada da duba masu lalurar ido da masu fama da cutar “dan dumi”, inda aka raba musu magunguna da kuma gilashi kyauta.

An tsara duba mutane 50 a kowacce mazaba cikin mazabu 15 da ke Karamar Hukumar Warawa, wanda hakan ya sa adadin wadanda suka amfana ya kai kimanin mutum 750.

Hon. Abdullahi Nasir Mai Kwano ya bayyana cewa ya gudanar da wannan aiki ne domin tallafawa al’umma da kuma rage musu wahalhalun rayuwa daidai gwargwadon abin da Allah Ya hore masa.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin sun bayyana farin cikinsu tare da godewa Hon. Abdullahi Nasir Mai Kwano bisa wannan aikin alkhairi da ya gudanar musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Matashin Da ‘Yandaba Suka Sare Masa Kafa Ya Nemi Taimakon Mahukunta

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa  Matashin nan mai suna Muh’d Abubakar Usman…

Gwamnatin Jihar Kano Zata Hada Hannu Da Gwamnatin Tarayya Domin Ciyar Da Harkokin Sadarwa Na Zamani A Fadin Jihar

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya…

Tarihi, Gwagwarmayar Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari Da Ya Rasu A Birtaniya

Daga: Sani Idris Maiwaya A cikin wani babban rashi da ya girgiza…

Tinubu Ya Saka Tiriliyan 3.3 Don Kawar da Duhu a Najeriya

Daga: Abdullahi Bashir Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani…