Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa 

Matashin nan mai suna Muh’d Abubakar Usman mazaunin unguwar Dorayi wanda ya rasa kafarsa guda daya sanadiyyar fadan daba da ya rutsa dashi.

Yau shekara daya da rabi kenan, yana kara rokon mahukunta da suyi masa adalci wajen bimasa hakkinsa akan zalincin da akai masa.

Muh’d yace, tun sanda wannan iftila’i ya fada masa suka kai batun gaban mahukunta. Cikin ikon Allah hukumar ta samu nasarar kama wasu daga cikin wadanda sukai wannan ta addancin.

Wanda hakan yasa muke tsammanin samun adalci game da zalincin da akaiwa wannan bawan Allah.

Sai dai har kawo yanzu Muh’d yace babu wani mataki gamsashshe da aka dauka akan wadan da suka shiga hannu.

A maimakon haka ma sai gashi wadanda ake zargin cutar da Muh’d sun fito daga hannun hukumar dake tuhumar tasun.

A lokacin dashi Muh’d ya rasa kafarsa guda daya an kassara masa rayuwarsa.

A don hakane yake rokon duk wanda zai iya shiga cikin al’amarin domin bi masa hakkinsa da ya taimakeshi ya sanya hannu cikin maganar

Muh’d yace, bayan faruwar wannan al’amari iyayensa da ‘yan uwansa sun shiga cikin matsananciyar damuwa mara misaltuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kungiyar sakwatawa da Zamfarawa da Kuma Kabawa Mazauna Jihar Kano da Jigawa ta jaddada kudirinta na tallafawa ‘ya’yan ta domin ganin sun dogara da Kawunansu. Shugaban kungiyar Alh

Kungiyar sakwatawa da Zamfarawa da Kuma Kabawa Mazauna Jihar Kano da Jigawa…

Sanata Barau Jibrin Zai Raba Wa Al’ummar Kano Ta Arewa Naira Miliyan 134.9 A Matsayin Kyautar Barka Da Sallah

Daga: Abdullahi Bashir Al’umma maza da mata na yankin Kano Ta Arewa suna…

Karamar Hukumar Dala Ta Kaddamar Da Aikin Hanyoyi Na Kimanin Miliyan 197 A Gobirawa

Daga: Sani Idris Maiwaya Karamar Hukumar Dala ta kaddamar da aikin hanya da…

A Ƙarshe: Gwamna Abba Yusuf Zai Koma APC Ranar Litinin

Kano – Ana ta rade-radin a ran Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf,…