Daga: Saminu Ibrahim Magashi

Masu saye da sayar da filaye a garin Rimin Zakara da ke Kano sun koka kan yadda suke zargin Kwamishinan Ƙasa na Jihar Kano da muzanta su tare da jefa su cikin rigingimu da abokan cinikayyarsu.

Shugaban dillalan filaye na Rimin Zakara, Alhaji Naziru Annatija, ne ya bayyana koken ’yan ƙungiyar, inda ya ce yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da lamarin na jefa dillalan cikin matsaloli tare da haddasa rashin jituwa tsakaninsu da mutanen da suka sayar wa filaye.

A nasa jawabin, wani daga cikin dillalan garin, Ishaq Abba Shawus, ya ce dillalan ba sa samun sukuni sakamakon yadda yake zargin Kwamishinan Ƙasa da ƙoƙarin haddasa rikici tsakaninsu da waɗanda suka sayar wa filaye.

Ya ce, duk da bayanin da Kwamishinan ya yi a gidajen rediyo cewa an biya kuɗin garin Rimin Zakara, dillalan sun bayyana cewa ba a biya su ko sisin kwabo ba, sai dai abin da suka ce ƙoƙari ne na ƙwace filayen al’umma masu ƙaramin ƙarfi.

Shi ma Alhaji Sulaiman Dangadi, shugaban ɓangaren Rijiyar Zaki, ya roƙi Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba lamarin tare da bincikar yadda ake tafiyar da al’amuran ƙasa a Rimin Zakara.

Alhaji Sulaiman ya ce gwamnati ya kamata ta kasance mai sasanta rigingimu tsakanin al’umma, ba wai ta zama sanadin ƙara haifar da su ba.

Haka kuma, wasu daga cikin masu mallakar filaye a Rimin Zakara sun bayyana damuwarsu kan abin da suka ce ƙoƙarin durƙusar da su da ƙwace musu filayensu, inda suka roƙi Gwamnan Kano da ya kawo musu ɗauki tare da tabbatar da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Matashin Da ‘Yandaba Suka Sare Masa Kafa Ya Nemi Taimakon Mahukunta

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa  Matashin nan mai suna Muh’d Abubakar Usman…

Mawuyacin Halin Da Makarantun Firamare Da Sakandire Na Langel A Ƙaramar Hukumar Tofa Ke Ciki

Daga:  Aliyu Ahmad Makarantun firamare da sakandire da ke ƙauyen Langel a…

Siyasar Ubangida Ita Ce Babbar Matsalar Da Ke Hana Najeriya Cigaba – Inji Comrade Nasiru Sulaiman Chamber

Daga: Kabir Getso Shugaban Hadakar Kungiyar Matasan Najeriya (United Nigeria Youth Congress), Comrade…

Matar Marigayi Buhari Ta Ziyarci Atiku A Saudiyya

Matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ta kai ziyara ga tsohon…