Daga: Sani Muhammad 

Kungiyar Masu Karɓar Fansho ta Najeriya ta ce an kafa ta ne domin kare jin daɗi da walwalar ‘yan fansho, da kuma tabbatar da cewa sun samu haƙƙoƙinsu.

Shugaban reshen ƙungiyar na Jihar Kano, Kwamared Shu’aibu Musa Jibril, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a Kano.

Ya ce shugabannin da suka gabata sun bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa da inganta tsarin fansho.

A cewarsa, manufar kafa ƙungiyar ita ce tabbatar da cewa ‘yan fansho sun samu alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin da suka cancanta.

Kwamared Shu’aibu ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin ‘yan fansho, tare da tabbatar da biyan kuɗaɗen fansho cikin lokaci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Remi Tinubu Ta Bukaci Burna Boy, Davido Da Asake Su Kafa Gidauniyoyi Don Taimaka Wa Talakawa

Daga: Sani Idris Maiwaya Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira…

Abinda Ya Sa Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Aiwatar Da Karin Kashi 40% Na Alawus Ga ASUU

Daga: Abdullahi Bashir Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da muhimman tanade-tanaden jin dadin…

Jami’ar Al-hikma Ta Bada Gurbin Karatun Mutum Uku Kyauta Daga Iyalan Mamatan ‘Yan Wasan Kano

  Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22…

Muna Samun Rashin Goyan Baya Daga Iyayen Matasa A Yakin Da Muke Da Matsalar Tsaro

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar rajin tabbatar da tsaro ta Tayani Mu…