Daga: Abdullahi Bashir
Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da muhimman tanade-tanaden jin dadin ma’aikata da ke cikin yarjejeniyar da aka sake tattaunawa da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), ciki har da alawus-alawus da suka shafi albashi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktar Yada Labarai da Hulda da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce fara aiwatar da shirin na nuna kudirin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, na cika yarjejeniyoyin da aka cimma da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi, tare da tabbatar da zaman lafiya a jami’o’in gwamnati.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya sanar da cewa gwamnati ta fara biyan karin kashi 40 cikin 100 na Consolidated Academic Allowance (CAA) ga mambobin ASUU, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Ma’aikatar ta tabbatar da cewa wasu jami’o’in tarayya sun riga sun fara nuna karin a cikin biyan albashin ma’aikata, yayin da ake daukar matakai domin tabbatar da cewa an aiwatar da shirin a dukkan jami’o’in tarayya ba tare da bambanci ba.
Sanarwar ta kara da cewa an sanar da jami’o’in tarayya a hukumance su shigar da karin cikin tsarin biyan albashinsu domin dukkan malaman da abin ya shafa su amfana.

Haka kuma, Ministan ya umurci shugabannin jami’o’i (Vice-Chancellors) da su tabbatar an bi ka’idojin aiwatar da Consolidated Academic Tools Allowance (CATA) yadda ya kamata, tare da jaddada muhimmancin amfani da kudade cikin hikima domin nasarar aiwatar da shirin.
Ya kara bayyana cewa Hukumar Albashi da Kudin Shiga ta Kasa (NSIWC) ta riga ta fitar da takardun da suka shafi biyan, kuma an tanadi kudin a cikin kasafin kudin shekarar 2026 bisa tsarin doka.
Ministan ya kuma bukaci hukumomin jami’o’i da su dauki matakai na gaggawa domin saukaka biyan alawus din cikin lokaci, yana mai cewa aiwatar da karin CAA da CATA zai kara karfafa yanayin koyarwa, bincike da koyo a jami’o’in Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudirinta na mutunta yarjejeniyoyi da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi, tare da ci gaba da inganta nagartar ilimi a fadin kasar.