Daga: Kabir Getso 

‎Khadija Leader Gwarzo me Gonar Gado ta Jika hantar mata ‘Yan Jam’iyyar APC A Gwarzo da tallafin kudi sama da Naira miliyan 5 da atamfofi 100.

‎Mataimakiya ta musamman ga Sanata Barau Jibrin Hon Khadija Lawan Gwarzo ta yi rabon kabakin arziki a yankinta na Gwarzo inda ta bayyana hakan a matsayin koyi ga Sanata Barau Jibrin

‎Sama da Mata Dari ne suka Rabauta da Atamfofi da kudade domin saukaka yanayin rayuwa da tallafawa al’ummar yankinta. Inda akayi robon cikin natsuwa da farin ciki ga wadanda suka amfana.

‎Hon Kadija Lawan  Gwarzo tace wannan rabon da tayi somin tabi ne domin zata cigaba da tallafawa al’ummar yankinta na Gwarzo domin farantawa mutanenta tare da  samun nasarar Jam’iyyar APC a yankin.

‎Tace duk da irin Tarin kungiyoyin mata da take dashi babu wani dan Siyasa ko Gwamnati da ya kirata domin bata wani tallafi da zata rabawa mata da take jagoranta, wanda tace hakan koma baya ne ga Cigaban Jam’iyyar APC a yankin.

‎Don haka take kira ga Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusif da ya duba lamarin wadanda ya kamata a rinka damkawa amanar mata a yankin Gwarzo domin isar da sakon gwamnatin ga al’ummar kai tsaye, sannan ta kara da cewar ya kamata a kira ta a zauna da ita domin jin irin korafin matan yankin.

‎”Wannan abu da nayi nayi ne da kudin aljihuna inda na kashe jimillar kudi Sama da Naira Miliyan 5 don tallafawa matan yankin namu” inja ta, Sannan tayi kira ga mata suyi amfani da tallafin ta hanyar da ya dace don cigabansu.

‎Hon Kadija Lawan Gwarzo ta yabawa Sanata Barau Jibrin bisa irin kokarin da yake ga al’ummar Kano ta arewa,wanda hakan ya zama abin koyi ga mu da muke tare dashi kuma hakan zai taimaka kwarai don samun nasarar Jam’iyyar APC a yankin da Jihar Kano Baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

’Yan Sanda Sun Kama Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Kano, Muhuyi Rimin Gado

Daga: Garba Hamza Yakasai ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban Hukumar Karbar…

2027: APC Ta Tsayar da Shettima A Matsayin Mataimakin Tinubu

Daga: Ibrahim Sani Gama Jam’iyyar APC ta tabbatar da ci gaba da…

Gwamnatin Mu Na Alfahari Da Gidauniyar Dangote

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi    Mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo…

Kungiyar Jami’an Tsaro Na Sa Kai Tana Taka Rawar Gani Ba Tare Da An Sanyasu A Tsarin Biyan Albashi Na Kasa

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar Jami’an Tsaro na Sa Kai ta Kasa reshen…