Daga: Mukhtar Yahaya Shehu
Halarar Sheikh Ibrahim Mai Tafsiri Kurmawa da ke cikin birnin Kano ta gudanar da taron Mauludin fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW kamar yadda ta saba gudanar wa duk shekara a Dararen 11 zuwa wayewar garin 12 da Kuma 18 zuwa wayewar garin 19 ga Watan Rabi’ul Auwal.
Taron zaman Mauludin Wanda ya ke gudana karkashin Jagorancin Khalifa Bashir Sheikh Ibrahim Mai Tafsiri Kurmawa ana gabatar da karatuttuka da jawaban kara Fadakar wa Kan al’amuran da suka shafi Addinin musulunci da Kuma kasidun yabon fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW.
Khalifa Bashir Ibrahim Mai Tafsiri a jawaban da ya gabatar a wayewar garin Talata 19 ga Watan Rabi’ul Auwal wato ranar Takutaha ya ja hankalin Al’uma Kan kara dagewa wajen neman Ilmi da Sanya Tsoron Allah cikin dukkanin Al’amura da Kuma kula wajen zaben shugabanni na gari musamman a daidai wannan lokaci da zabe ke kara karatowa.
A bangaren neman Ilmi khalifa Bashir Ibrahim ya bayyana shi a matsayin fitilar haskaka rayuwa ta fuskar sanin yadda za a bauta wa Allah madaukakin Sarki.
A bangaren yin aiki da ikhlasi kuwa, khalifa Bashir Ibrahim ya bayyana shi a matsayin hanyar da za ta kara kusanya bawa ga Mahaliccin SA ba tare da Sanya Riya ba.
Khalifa Bashir Ibrahim Mai Tafsiri Kurmawa ya ja hankalin Al’uma Kan kara kula wajen zaben shugabanni na gari bisa cancanta kasancewar ‘yan siyasa na amfani da wannan lokaci wajen karkatar da hankulan Al’uma idan zabe ya karato da Dan abin da bashi da yawa wajen samun nasara.
” Ya kamata a kula kada wani mai neman kuri’ar ka da bai cancanta ba idan zabe ya karato ya baka Dan abin da bashi da yawa da ba zai ishe ka cin abinci rana guda ba ka sayar da ‘yancin ka na tsawon Shekaru ba.” In ji Khalifa Bashir
Taron zaman Mauludin na fiyayyen Halitta na Halarar Sheikh Ibrahim Mai Tafsiri Kurmawa daga cikin littattafan yabon fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW akwai Tani’a da Anwarul Muhammadi da Fairal Ahmadi da Kuma Saukar karatun Alkur’ani mai tsarki.
Taron zaman Mauludin yana bin sahun sauran manyan Halarar gidajen manyan malaman Addinin musulunci da ke nan kano a dukkanin Dararen 11 da sha 18 da sauran kwanakin Watan Rabi’ul Auwal a duk shekara.