Daga: Tanimu Salihu
Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta fara gudanar da bincike kan yadda ake aiwatar da manufar amfani da iskar gas mai matsewa (CNG) a Najeriya.
A wajen kaddamar da kwamitin na wucin gadi da ke kula da binciken aiwatar da manufar CNG a birnin Abuja, Shugaban kwamitin, Hon. Ahmadu Jaha, ya bayyana cewa za su tantance tsaron lafiyar, dacewa da dorewar wannan manufa a fadin ƙasar nan.
A cewar Jaha, kwamitin zai tabbatar da cewa bangaren zartarwa na gwamnati ya samar da cibiyoyin CNG a kowane yanki na ƙasa domin bai wa ‘yan Najeriya damar jin daɗin mallakar wannan tsari.
Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa za su tuntubi hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki, kamfanonin mai na ƙasa da na ƙetare (IOCs) da kuma sauran ƙungiyoyi domin tabbatar da cewa manufar Najeriya kan CNG ta dace da ƙa’idojin duniya.
Ya bayyana cewa za su duba ko dokoki da ƙa’idojin da ke akwai sun isa wajen tafiyar da wannan manufa, tare da bayar da shawarwari kan yadda majalisa za ta ɗauki matakan doka domin ƙarfafa tsarin.

Hon. Jaha ya nuna godiyarsa ga shugabancin majalisar bisa haɗa kwamitin, yana mai cewa an haɗa shi ne da ‘yan majalisa masu ƙwarewa, jajircewa da kishi wajen gudanar da ayyukansu.