Fataccen Dan kasuwa kuma shugaban kamfanin gine-gine na SKY construction limited Alhaji kabiru sani kwangila yakasai khadimun Nabiyyi ya nuna matuƙar alhini kan rasuwar fitattun yan kasuwa Alhaji Bature Abdulaziz, da Alhaji idi Balarabe wadanda suka rasu a kano.

 

Sky ya bayyanasu a matsayin wadanda suka bada gagarumar gudunmawa a harkokin kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki, inda ya ce gudunmawar da suka bayar za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a Kano da kasa baki ɗaya.

 

Sky Ya kuma miƙa sakon ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kano da kuma iyalan Fatima Abubakar, wadda wasu bata gari suka kashe tare da ’ya’yanta guda shida a unguwar Dorayi Chiranchi,dake Karamar Hukumar Kumbotso.

 

Sky ya kuma yi Allah-wadai da wannan mummunan aiki, yana mai kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su gaggauta bincike tare da tabbatar da cewa duk masu hannu a laifin sun fuskanci hukunci bisa doka.

 

Ya kuma mika sakon taaziyya ga iyalan Alhaji Dallami Alasan bisa rasuwar Dansa sadik Danlami Alasan .

 

Ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya jiƙan mamatan da rahama, Ya kuma ba iyalan da suka rasa nasu ƙarfin jure wannan babban rashi da sauran alummar musulmi baki daya.

 

Cov kamal yakubu Ali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Likitocin Da Ƙasa Ta Horar Kada Su Bar Ta Cikin Ƙunci — Dr. Habib

Daga: Kabir Getso  ‎Akwai Bukatar likitoci su daina kwarara zuwa kasashen ketare…

Za a Kashe Ɓeraye Domin Dakile Yaduwar Cutar Lassa- Gwamnatin Kano

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta…

KSPHCMB Ta Tsaurara Mataki Kan Sakaci, Ta Ba Masu Ƙwazo Lambar Yabo

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu The Director General of the Kano State Primary Health…

Shugaban Karamar Hukumar Kura Ya Mika Gudunmawar Gaggawa Ga Babban Asibiti – Hon. Rabi’u

Daga: Dantala Uba Nuhu Alh Rabiu Abubakar Suleman Babina ya mika gudunmawar…