Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na samar da ingantattun kayayyakin koyo da koyarwa domin habaka harkar ilimi a manyan makarantun da ke fadin jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ne ya bayyana hakan yayin da tawagar jami’ar North West, karkashin jagorancin sabuwar shugabarta Farfesa Amina Salihi Bayero, suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.
Kwamared Gwarzo ya bayyana farin cikinsa kan nadin Farfesa Amina Salihi Bayero a matsayin shugabar jami’ar, inda ya bayyana cewa an dora amanar a hannun kwararriya wadda ta dace da mukamin. Ya kuma ba da tabbacin cikakken goyon bayan gwamnatin Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wajen daga martabar jami’ar domin ta yi gogayya da sauran jami’o’i a fadin kasar nan.

A jawabinta, shugabar jami’ar, Farfesa Amina Salihi Bayero, ta nuna jin dadinta kan yadda gwamnatin jihar ke bai wa ilimi muhimmanci, tare da jinjina wa manufofin da suka shafi bunkasa manyan makarantu.

Ta bayyana cewa makasudin ziyarar shi ne gabatar da kanta a hukumance, tare da mika kudirori da bukatun jami’ar ga gwamnatin jihar domin samun hadin kai da goyon baya. Haka kuma ta gode wa Mataimakin Gwamnan bisa jajircewarsa wajen tabbatar da jami’ar ta samu tsayayyen matsayi.

Taron ya samu halartar mambobin majalisar gudanarwar jami’ar, da Babban Sakataren Ofishin Mataimakin Gwamna, da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano: Ƙofarmu A Buɗe Take Domin Karɓar Shawarwari — Mataimakin Gwamna

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…

Mataimakin Gwamna Ya Gana Da Karamin Ministan Gidaje A Abuja

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Karamin ministan gidaje da raya birane Rt. Hon.…

Ta’aziyya: Rasuwar Galadima Babban Rashi Ne A Masarautar Kano- Sanka

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu An bayyana rasuwar marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi…

Yunkurin Juyin Mulki A Najeriya Abin Takaici Ne — Zangina

Daga: Kabir Getso Shugaban ƙungiyar Grassroot Mobilization for Tinubu 2027, Alhaji Sani…