Daga: Garba Musa Hamza

Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana shirin gina wasu sabbin matatun tace ruwa guda biyu, domin ƙara samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’ummar jihar.

Manajan Daraktan Hukumar Samar da Ruwa ta Kano, Injiniya Ahmad Garba Bichi, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar duba ayyuka a matatar tace ruwa ta yankin Wudil, tare da mai bai wa Gwamna shawara kan yaɗa labarai, Honarabul Ahmed S. Aruwa, da tawagarsa.

Injiniya Bichi ya ce Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Dakta Dahiru Hashim, na aiki kan tsarin sabbin ayyukan, wanda za a miƙa wa Gwamna Abba Kabir Yusuf domin amincewa.

Ya bayyana cewa matatar tace ruwa ta Wudil tana da rijiyoyin burtsatse guda goma sha tara, amma guda huɗu ne kawai ke aiki a halin yanzu.

A cewarsa, matatar tana samar da ruwa ga ƙananan hukumomin Wudil, Gaya da Dawakin Kudu bisa tsarin juyawa.

Ya kuma ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin haƙa ƙarin rijiyoyin burtsatse guda biyar, domin ƙara ƙarfin samar da ruwan tare da kai shi Hotoro da kewaye a cikin birnin Kano.

Manajan Daraktan ya kuma nuna damuwa kan kwashe yashi ba bisa ka’ida ba da wasu ke yi, da kuma kasancewar matsugunan Fulani a kusa da matatar, yana mai cewa waɗannan ayyuka na iya yin barazana ga samar da tsaftataccen ruwan sha.

A nasa bangaren, mai bai wa Gwamna shawara kan yaɗa labarai, Honarabul Ahmed S. Aruwa, ya bayyana gamsuwarsa da abin da ya gani a matatar tace ruwa ta Wudil.

Aruwa ya tabbatar wa jama’a cewa ofishinsa zai ci gaba da wayar da kan al’umma kan ci gaban da gwamnatin jihar ke samu wajen inganta samar da ruwa.

Ya ce masana’antar tace ruwa ta Wudil tana aiki yanzu, kuma akwai ruwan sha a garin Wudil.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kungiyoyin Matuka Motocin Kurkura Da Na Manyan Motoci Sun Yi Alwashin Tallafawa Tsaftace Muhalli

Daga: Ibrahim sani Gama Kungiyar matuka motocin korkura ta jihar Kano da…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Dr. Gawuna Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Madakin Gini da Likita

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Kuma Shugaban hukumomin gudanar…

Gwamnatin Jihar Kano Ya Jaddada Aniyarta Wajen Bunkasa Ilimin Fasaha A Fadin Jihar

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo,…

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Ya Kai Ziyarar Jajantawa Asibitin Malam Aminu Kano

Daga: Shehu Suleiman sharfadi Mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…