Daga: Mas’ud Mato Garo

Mataimakin gwamnan kanon ya bayyana hakan ne yayin da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron bita kan aiwatar da dokar kare bayanai, wanda Ƙungiyar Gwamnoni ta Ƙasa (NGF) ta shirya tare da Hukumar Kare Bayanan ‘Yan Ƙasa (NDPC) a Abuja.

Alhaji Murtala Sule Garo ya jaddada cewa bayanan al’umma na daga cikin muhimman abubuwa da gwamnati ke bukata wajen tsara manufofin ci gaba, don haka akwai bukatar ba su cikakkiyar kariya a koda yaushe.

Ya kara da cewa kare bayanan na ’yan ƙasa nauyi ne na kowa, inda ya buƙaci jami’an gwamnati su kula da tsaron bayanan jama’a tare da kiran gwamnatoci su riƙa shirya tarukan horas da ma’aikata a kai a kai.

A yayin taron, Mataimakin Gwamnan na tare da Babban Daraktan Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano (KASITDA), Dr Bashir Muzzakkar, da Mai Ba Gwamna Shawara kan Tattalin Arzikin Zamani, Malam Yusuf Ibrahim Sharada, da sauran wakilan jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano Za Ta Gina Sabbin Matatun Tace Ruwa Biyu

Daga: Garba Musa Hamza Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana shirin gina wasu…

Gwamnatin Kano Ba Za Ta Lamunci Yanka Fulotai Ba Tare Da Izini Ba – Kwamishina Abduljabbar

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudurin ta na rushe…

Muhimmancin Tsaro Da Kare Dukiyoyin Al’umma – Kwamared Saminu

Daga: Dantala Uba Nuhu Kura Babban kwamitin cigaban tsaron al’ummar ‘Yan-Danko dake…

Zamu Baiwa Gwamnatin Jihar Kano Baya Domin Samarwa Matasa Sana’o’in Dogaro Kai

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar matasan yankasuwa dake kasuwar Singa ta bayyana…