Daga: Mukhtar Yahaya Shehu
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudurin ta na rushe duk wani gini da aka yi ba bisa ka’ida ba ko kuna yanka Fulotai ba tare da izini ba.
Kwamishinan kasa da tsare -tsare na jihar Kano Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ne Ya sanar da haka yayin da ya jagoranci rushe wasu gine -gine da filaye da aka yanka ba tare da Izini ba a garin watari tsohon gari da ke karamar hukumar Kumbotso.

Ya ce sun ziyar ci yankin ne bayan korafin da al’umar yankin suka kai cewa wasu bata-gari suna yanka filaye a gefen Gadar da ke yankin Wanda har ta Kai sun fara yi wa Gadar illa.
Kwamishinan ya ce sun gamsu wadannan filaye an yanka su ba tare da Izini ba, Wanda Kuma ma’aikatar kasa ta rushe su.

“Wannan Gadar da ke wannan gari na watari ta ta tashi ne tun daga Janguza ta hade da Karaye har zuwa Karamar hukumar Rogo da aka yi ta shekaru 50 da suka gabata wadda mafi yawa nanoma da makiyaya ne suka fi amfani da ita, Amma Sai gashi wasu marasa kishin kasa suna yi mata illa ta hanyar yanka filaye ba tare da Izini ba.” In ji kwamishina Abduljabbar
Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar ya kara jaddada kudurin gwamnatin jihar Kano na cigaba da daukar irin wannan mataki domin daidaita taswirar jihar.

A yayin waccan ziyar dakatar da wadancan Bata -gari al’umar yankin sun nuna farin cikin su bisa wannan mataki da ma’aikatar kasa da tsare -tsare ta jihar Kano ta daukar.