By: Mukhtar Yahaya Shehu
A ranar Litinin, 23 ga Maris, 2026, Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiya na Matakin Farko ta Jihar Kano Professor Salisu Ahmad Ibrahim, ya kai ziyara ta gaggawa a Cibiyar lafiya ta Farko da ke Kabuga (PHC) domin duba ayyukan ma’aikata da inganta ingancin kula da lafiya a fadin jihar Kano.
A cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a wato Sa’adatu Sulaiman ta saka hannu, Darakta Janar ya nuna damuwa kan rashin zuwan ma’aikata aiki da kuma rashin kiyaye lokutan aiki, wanda hakan ke kawo cikas ga ingantaccen aikin ta hukumar dake Kabuga.
A matsayin mataki na gaggawa don dawo da oda da inganci, Professor Ibrahim ya sauke mukamin mataimakiyar jami’ar cibiyar daga aiki, inda ya nada Khadija T. Musa a madadinta wadda aka bayyana da jajircewa da kiyaye lokaci.
Haka kuma, sashen Rigakafin Yara (Routine Immunization – RI Unit) ya samu sabon tsarin shugabanci bayan an gano matsalolin gudanarwa. An maye gurbin jami’in sashen da Maimuna Adnan Abdulhamid domin tabbatar da kyakkyawar hadin kai da karfafa ayyukan rigakafi a cibiyar.
Bugu da kari, an bai wa sauran ma’aikatan cibiyar takardun gargaɗi kan rashin bin lokutan aiki. Professor Ibrahim ya sake jaddada tsananin hukunci kan rashin ladabi, tare da bayyana muhimmancin ladabi, himma, da kwarewa wajen bayar da ingantaccen kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Kano.