Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin Tarayya ta magantu a yayin da ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa yaɗa labaran da ke nuni da nasarorin da Najeriya ta samu a tsarin mulkin dimokiraɗiyya.

Alhaji Mohammed Idris Wanda ya kasance Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ne ya bayyana hakan a yayin bikin cikar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) shekaru 70 da kafuwa, wanda aka gudanar a cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da ke birnin Tarayya Abuja.

An ƙaddamar da wani littafi na tarihin ƙungiyar tare da kuma haɗawa da karramawa.

 

Ministan da yake jawabi a matsayin Babban Baƙon a wannan taron, Bisa wakilcin Shugaban Ƙasa Tinubu, kuma a matsayin Jagoran Biki, ya jaddada kusanci da goyon bayan da Shugaba Tinubu yake da shi ga kafafen yaɗa labarai a ƙasar nan.

Inda ya ce: “tun daga lokacin da ya kasance cikin masu gwagwarmayar tabbatar da zaɓen watan Yuni 12 tare da jarumai daga cikin ‘yan jaridu, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya kafa dangantaka mai ƙarfi da kafafen yaɗa labarai wanda ba a taɓa ganin makamancin sa a tarihin shugabannin Ƙasarnan ba.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

A Shirye Muke Mu Yi Aiki da Kungiyar Matan 12 Pillars – Hon. Surajo Imam

Daga: Sani Idris Maiwaya DALA, KANO – Shugaban Karamar Hukumar Dala, Alhaji Surajo…

Jaridar BusinessDay ta karrama Gwamnan Jihar Kano da lambar yabon Business Governor of the Year.

Daga Mas’ud Mato Garo Mataimakin gwamnan kano Murtala Sule Garo ne ya…

Sojojin Najeriya Sun Halaka ‘Yan Ta’adda Takwas a Borno

Daga: Hamza Garba Yakasai Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun…

Kwamatin Tsaro na Majalisar Karamar Hukumar Dala ya Haramta Dunkannin Wani Taron Gangi, ko kidan Tauri Dama Duk Wani taro akan hanyar da Al’umma Ke wucewa a Fadin Karamar Hukumar Dala

Kwamatin Tsaro na Majalisar Karamar Hukumar Dala ya Haramta Dunkannin Wani Taron…