Daga: Kabiru Getso

Shugaban Kwalejin koyar da aikin gona ta Audu Bako da ke karamar hukumar Dambatta, Farfesa Muhammad Audu Wailare, ya musanta zargin da ake yi wa kwalejin na kin bin umarnin gwamnatin Jihar Kano.

A yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa, Farfesa Wailare ya bayyana cewa, labaran da ke yawo cewa kwalejin ta bijirewa umarnin gwamnati, kan dakatarwar da aka yi wa wani malami, Malam Ahmad, bisa zargin duka da ya yi wa wani abokin aikinsa a bainar jama’a, ba gaskiya ba ne.

Farfesa Wailare ya ce, shugaban kungiyar malaman kwalejojin kimiyya da fasaha na kasa, reshen Arewa maso Yamma, Dakta Abdul’aziz Badaru, ne ke yada labaran kanzon kurege da nufin bata sunan kwalejin da kuma karkatar da gaskiya.

“Dakta Badaru yana amfani da kafafen yada labarai wajen yada bayanan da ba su da tushe, yana cewa mun ki bin umarnin gwamnatin Jihar Kano, alhali kuwa mun bi duk matakan da doka ta tanada wajen dakatar da Malam Ahmad,” in ji Wailare.

Ya ce gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf ce kadai a tarihin kwalejin da ta bai wa cibiyar kulawa ta musamman wajen bunkasa harkokin ilimi da ci gaban kwalejin.

Farfesan ya bayyana cewa, “Tun lokacin da na hau shugabancin wannan kwaleji, babu wata gwamnati da ta ba mu kulawa da tallafi kamar wannan gwamnatin mai ci. Don haka wajibi ne mu yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa irin kokarin da yake yi wajen inganta harkar ilimi a fadin jihar Kano.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Silar Karancin Gandaye Wannan Azumin – Hisbah

Daga: Jamila Suleiman Aliyu  Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yabawa iyaye da…

Al’umar Unguwar Gobirawa Sun Bukaci Dan Majalisa Ya Kammala Musu Hanya

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Al’ummar Gobirawa Sun Bukaci Alhaji Aliyu Sani Madakin Gini…

Ganawar Al’ummar D/Kudu da Kwankwaso: Har Yanzu Shi Ke Da Jama’ar Kano – Hon. Abdulmumin Tijjani Mai POS

Daga: Kabir Getso Tsohon ɗan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Dala/Kudu…

Hakimai Sunyi Mubayi’a Ga Shugaban Karamar Hukuma

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu   Shugaban karamar hukumar Birnin Kano Alhaji Salim…