Daga: Kabir Getso
Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da unguwarzoma ta kasa, reshen Jihar Borno, Kwamared Muhammad Yaro, wanda mataimakinsa Kwamared Sa’idu H. Gwalan ya wakilta, ya jinjinawa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, kan matakan da yake dauka don inganta walwalar ma’aikatan lafiya a jihar.
A ganawarsa da manema labarai, Kwamared Gwalan ya bayyana cewa babu shakka gwamnatin jihar ta yi abin yabo musamman wajen aiwatar da sabon tsarin albashi da zai kara inganta sha’anin lafiya da bunkasa ma’aikatan jinya da unguwarzoma.

Ya ce kungiyar ta samu damar tattaunawa da Gwamna Zulum, inda ta gabatar masa da matsalolin da suke addabar ma’aikatan ciki har da karancin jami’an lafiya, rashin wadatattun kayan aiki da kuma rashin gamsasshen albashi. A cewarsa, Gwamnan ya ba da tabbacin cewa gwamnati na kan hanyoyin shawo kan wadannan matsaloli.
Haka kuma ya yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da daukar karin ma’aikatan lafiya domin karancin su na kawo tangarda ga tsarin kula da lafiya a jihar.
Kwamared Gwalan ya kara da cewa nan gaba kadan gwamnatin jihar za ta dauki matakan dakile yawan kwararar ma’aikatan lafiya zuwa wasu jihohi da kasashen waje domin neman aiki, maimakon su tsaya su yi hidima a Borno.

Daga karshe, ya bukaci dukkan ma’aikatan jinya da ungozoma da su dage wajen gudanar da aikinsu cikin jajircewa da kishin kasa, domin ci gaban lafiya a jihar.
