Daga: Kabir Getso
Shugaban Husaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure, Engr. Dr. Bashir Ahmad Danzomo, ya bayyana cewa kwalejin na alfahari da ɗalibanta a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar, sakamakon jajircewa da tsayin daka da take yi wajen koyarwa da ilmantar da ɗalibai.
Danzomo ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan yadda kwalejin ke gudanar da ayyukanta, inda ya ce makarantar na da Sassa shida masu koyar da kwasa-kwasai daban-daban, tare da ƙwararrun malamai da suka samu horo na musamman domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai.

Ya ƙara da cewa tun bayan da ya karɓi ragamar shugabancin riƙon kwalejin, ya samu haɗin kan malamai wajen gano matsalolin da ke damun makarantar da kuma magance su cikin ƙanƙanin lokaci. Daga cikin ayyukan da aka fara akwai ƙarin ɗaukar ma’aikata musamman a ɓangaren tsaro, gyare-gyare a harabar kwalejin, samar da isasshen ruwan sha ga ɗakunan kwanan ɗalibai da tsaftace muhalli domin samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyarwa.
Shugaban kwalejin ya kuma yaba wa Sanata Babangida Husaini, Walin Kazaure, bisa tallafin da yake bai wa kwalejin, musamman gina wani katafaren ɓangare na makarantar tare da samar da kayan aikin da ake buƙata. Ya kuma yaba wa shugabannin ƙananan hukumomin Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi bisa ɗaukar nauyin wasu ɗaliban yankunansu domin samun ilimi a kwalejin.

Danzomo ya yi kira ga sauran al’umma, musamman masu hannu da shuni, da su ci gaba da tallafa wa ilimin matasa, yana mai cewa zuba jari a ilimi zai taimaka wajen rage rashin aikin yi da kuma magance barazanar tsaro a tsakanin al’umma.