Daga; Abdullahi Bashir
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake lashe zaben gwamnan jihar, inda ya samu nasarar komawa kan kujerar na wa’adin karo na biyu.
Adeleke, dan takarar jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, yayin da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya samu kuri’u 444,815.

Dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180.
Jami’in zaben na INEC, Farfesa Joshua Ogunwole, ne ya bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Osogbo, babban birnin jihar, a safiyar yau Lahadi.
Adeleke ya samu nasara a kananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11.

Wannan nasara ta bai wa Adeleke damar ci gaba da jagorantar Jihar Osun na karin wa’adin shekaru hudu a karo na biyu.