Daga: Ibrahim Sani Gama
Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa kiran waya da ya yi masa tare da taya shi murnar samun nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar jiya Asabar.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ayyana Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun ƙuri’u 511,067, inda ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya samu ƙuri’u 444,815.

Adeleke, yayin da yake magana bayan sanar da sakamakon zaɓen, ya bayyana nasarar a matsayin cikakkiyar dimokuraɗiyya ga al’ummar Osun.
Ya ce: “Ina amfani da wannan dama wajen gode wa Mai Girma Shugaban Ƙasa. Shugaban Ƙasa ya kira ni ya taya ni murna. Na godewa, Shugaban Ƙasa, saboda tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da wanzuwa.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa nasarar tasa ta nuna amincewar al’ummar jihar da ayyukan gwamnatinsa, musamman a fannonin samar da ababen more rayuwa, kiwon lafiya da tsaro.

Adeleke ya samu nasara a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji ya samu nasara a ƙananan hukumomi 11, abin da ya bai wa gwamnan tazarar ƙuri’u 66,252.
Haka kuma, Adeleke ya yi kira da a duba zaɓen a matsayin nasara ga kowa, yana mai cewa babu wanda ya yi rashin nasara, kuma yana fatan abokin hamayyarsa zai kira shi domin taya shi murna.