Daga: Saminu Ibrahim Magashi

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba wa ƙoƙarin ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Kano Capital wajen farfaɗo da martabar makarantar da kuma tallafa mata domin ci gaban harkar ilimi.

Da yake jawabi a yayin bikin cikar Makarantar Kano Capital shekaru 35 da kafuwa, Sarkin Kano ya bayyana ilimi a matsayin muhimmiyar hanya ta kawo gyara a cikin al’amuran rayuwa. Ya kuma yi alƙawarin haɗa kai da masu ruwa da tsaki domin ganin an dawo da martabar makarantar kamar yadda take a baya.

 

A nata jawabin, shugabar kwamitin shirya taron, Barrister Faiza Dahiru Sidi, ta ce manufar shirya taron ita ce duba halin da makarantar ke ciki, musamman yadda ta koma baya, tare da tattaro tsofaffin ɗaliban makarantar domin kawo mata agajin gaggawa.

 

Ta ƙara kira ga tsofaffin ɗaliban da su ci gaba da ba makarantar cikakken goyon baya domin samun damar inganta yanayin karatu da koyarwa.

 

Haka kuma, Dr. Surayya Ado Bala ta bayyana cewa ƙungiyar ta tallafa wa makarantar da teburan zama guda 150 da allunan rubutu guda shida, tare da gyaran bandakuna. Ta ce an kuma tallafa wa ƙananan ma’aikatan makarantar da kuɗi da kayan abinci.

Ita ma shugabar sashen mata na Makarantar Kano Capital ta nuna matuƙar godiya ga tsofaffin ɗaliban bisa irin tallafin da suka bayar, tana mai cewa ba kasafai ake samun irin wannan haɗin kai da taimako ba.

Ta ƙara da cewa tsofaffin ɗaliban sun yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin makarantar ta dawo hayyacinta da martabarta ta baya.

Shugabar ta kuma yaba wa ƙoƙarin Gwamnatin Jihar Kano wajen tallafawa harkar ilimi da kuma ƙoƙarin inganta fannin ilimi a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyyar APC a Madobi Sun Jaddada Goyon Bayansu ga Dukkan ‘Yan Takarar Jam’iyyar – Hassan

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Madobi sun…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano, Gawuna, Ya Sauya Jam’iyya

Daga: Hamza Musa Yakasai Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasir Yusuf Gawuna, ya…

Nuna Alhini Kan Rasuwar ‘Yan Wasan Kano 21 A Gasar Wasanni Ta Kasa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Bayero Kano kuma Shugaban…

Masu Buƙata Ta Musamman A Kano Sun Koka Kan Rashin Samun Tallafin Gwamnati

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugabancin Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa Masu Buƙata ta Musamman ta…