Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Madobi sun sake jaddada aniyarsu ta tsayawa tsayin daka wajen marawa dukkan ‘yan takarar jam’iyyar APC baya, tun daga matakin Shugaban Ƙasa har zuwa na ƙananan mukaman siyasa.

Hakan ya fito ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar inda aka tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin kai da tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.

Da yake jawabi a wajen taron, Jagora a karamar hukumar, Alhaji Habibu Hassan El-Yakub ya buƙaci mambobin jam’iyyar su kasance masu haɗin kai da biyayya ga shugabanni, yana mai cewa nasarar APC za ta samu ne idan aka kauce wa rarrabuwar kai tare da bai wa dukkan ‘yan takara cikakken goyon baya.

A nasa jawabin,Jigo a jamiyyar APC Dr. Musa Ilyasu Kwankwaso ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin mambobin jam’iyyar, yana mai kira ga kowa da ya yi aiki tukuru domin ganin APC ta samu gagarumar nasara a dukkan matakan zaɓe mai zuwa.

Anasa jawabin shugaban karamar hukumar Madobi Hon. Suleiman Dan Azumi ya yabawa masu ruwa da tsakin jam’iyyar bisa jajircewarsu da kuma matsayar da suka ɗauka ta marawa dukkan ‘yan takarar APC baya. Ya kuma yi kira ga matasa, mata da sauran magoya baya da su ci gaba da gudanar da siyasa cikin lumana da mutunta dokokin jam’iyya.

A yayin taron, masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun tabbatar da Hon. Suleiman Mukhtar a matsayin ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Kura Madobi, Garin malam da Hon.Yahaya Musa Kwankwaso a matsayin ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Kano, inda suka bayyana cikakken goyon bayansu gare su.

A jawabansu, daban daban Hon. Suleiman Mukhtar dan takarar majalisar tarayya kura Madobi Garin malam da Hon.Yahaya Musa Kwankwaso dan takarar majalisar Jaha sun nuna matuƙar farin cikinsu da amincewa da goyon bayan da aka ba su. Sun yi alƙawarin yin siyasa ta haɗin kai, adalci da kusanci da al’umma, tare da wakiltar muradun al’ummar mazabunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

YABO DA KIRA: Shugaban APC na Giginyu Ya Jinjinawa Gwamna Abba, Ya Nemi A Gyara Gadar Badawa

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban ƙungiyar Giginyu Peace kuma Shugaban jam’iyyar APC na…

Dangote Ya Rage Farashin Fetur, Ya Kaddamar da Sabon Tsarin Rarrabawa

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Kamfanin matatar mai na Dangote ya saukar da…

Ta’aziyya: Rasuwar Galadima Babban Rashi Ne A Masarautar Kano- Sanka

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu An bayyana rasuwar marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi…

Ed el Adha: Shugaban K/H Birnin Kano Ya Yi Wa Al’umar Musulmi Barka Da Sallah

By: Mukhtar Yahaya Shehu Shugaban karamar hukumar Birnin Kano Alhaji Salim Hashim Gwangwazo…