Daga: Abdullahi Bashir

Babban Ministan Kudi na ƙasa, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta tsoma baki wajen kayyade farashin fetur ba duk da tashin hankali da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ke janyo sauyin farashin mai a kasuwannin duniya.

Edun ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Gidan Telebijin din Channels a daren jiya Laraba.

Ya ce maimakon gwamnatin ta kayyade farashin fetur, tana shirin bullo da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen rage tasirin yakin kan siyasar duniya na tattalin arzikin Najeriya da rayuwar al’umma.

Ministan ya ƙara da cewa, tuni Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da samar da ƙarin kayan sauya motoci zuwa amfani da iskar Gas guda 100,000 domin bai wa masu motoci damar komawa amfani da iskar Gas din.

A cewarsa, amfani da CNG yana da araha sosai, domin farashinsa yana tsakanin kashi 25 zuwa 30 cikin 100 na farashin fetur, abin da ake sa ran zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da kuma sauƙaƙa wa jama’a nauyin hauhawar farashin mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Pyramid Radio Za Ta Hada Hannu Da Jami’ar Maryam Abacha Don Inganta Aikin Jarida A Kano

Daga: Yakubu Abubakar Gwagwarwa Gidan Radio tarayya Pyramid FM zai hada hannu…

Mun ji Dadin Sake Bude Tashar Manyan Motoci Ta Dakatsalle – Zainawa

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugabancin kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen…

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani sabon mataki da zai shafi dukkan…

Hukumar Kula Da Lafiya Matakin Farko Ta Dakile Rashin Ladabi, Ta Sake Tsarin Shugabanci A  Kabuga

  By: Mukhtar Yahaya Shehu A ranar Litinin, 23 ga Maris, 2026,…