Daga: Garba Hamza Yakasai

Tsohon gwamnan jihar Sokoto State kuma Sanata mai wakiltar Sokoto South Senatorial District, Aminu Waziri Tambuwal, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da komawa jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a hukumance.

Tambuwal ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Maris, 2026, wadda ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na mazabarsa, inda ya ce ya fice daga jam’iyyar nan take.

Sanatan ya kuma sanar da cewa shi da magoya bayansa sun shiga jam’iyyar ADC, yana mai jaddada cewa ya ɗauki matakin ne bisa imaninsa cewa Nigeria na buƙatar tsarin siyasa mai ƙarfi da ya ginu kan gaskiya, riƙon amana da haɗin kai, domin samar da ingantaccen ci gaba ga ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Kano Ta Kama Wadanda Ake Zargi Da Yanka Filaye ba bisa ka’ida Ba A Gundutse Trailer Park

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudurin ta na…

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yabawa Kungiyar Tsoffin Kansiloli

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin jihar Kano ta yabawa kungiyar tsofaffin kansiloli…

Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Dr. Gawuna Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Madakin Gini da Likita

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Kuma Shugaban hukumomin gudanar…

Dalilin Da Ya Sa Atiku Bai Halarci Taron G-100 Ba — ADC

Daga: Abdullahi Bashir Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana dalilin da…