Daga: Kabir Getso 

Shugaban Karamar Hukumar Taura, Hon. Dr. Shua’ibu Ibn Hambali, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba al’ummar yankin za su shaida gagarumin ci gaba, musamman ta fuskar ayyukan raya kasa da tallafin da ake bai wa masu zalla wajen inganta cigaban al’umma.

Yayin ganawarsa da manema labarai, Dr. Hambali ya ce kusancin da shugabannin kananan hukumomi ke da shi da al’umma yana ba su damar fahimtar matsalolin jama’a kai tsaye, lamarin da ya sa ayyukan da suke aiwatarwa ke samun karɓuwa da goyon baya daga kungiyoyin cigaba da shugabannin al’umma.

A cikin dan lokaci, shugaban ya kaddamar da muhimman ayyuka a Taura da kewaye, wadanda suka haɗa da gyaran tituna, inganta hanyoyin sadarwa da kuma tallafa wa makarantun boko da islamiya. Daya daga cikin manyan ayyukan da ya kammala kwanan nan shi ne cika alkawarin sayen filin da ya kai kimanin naira miliyan 2.5 ga makarantar Bakin Dogo Islamic School, domin kara habaka ilimi a yankin.

Dr. Hambali ya bayyana cewa gwamnatin karamar hukumar na aiwatar da wadannan shirye-shirye ne a matsayin daukar darasi daga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda ya dage wajen ganin an samu cigaba a jiha, musamman a fannonin hanyoyi da ruwa.

A cewar sa, gwamnatin jihar ta ware N292 miliyan domin gina sabbin na’urorin samar da ruwa ta hasken rana a yankuna 19, tare da N81 biliyan na inganta tituna masu tsawon makudan kilomitoci don kara ɗaga darajar tattalin arzikin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

K/H Safana: ‘Yan Kasuwa Sun Nemi Gwamnati Ta Shiga Lamarin Rusau

Daga: Ibrahim Sani Gama Al’ummar ‘yan kasuwar Tsaye da ke ƙaramar hukumar…

Gwamna Adeleke Ya Sake Lashe Zaben Gwamnan Osun

Daga; Abdullahi Bashir Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake lashe zaben gwamnan…

Hukumar Kare Hakkin Mai Siye Da Siyarwa:Mun Yi Nasarar Dakile Kayan Da Suka Lalace Da Dama A Jihar Kano

  Daga: Adamu Dabo Hukumar kare Hakkin Mai siye da siyarwa ta…

Mataimakin Gwamnan Kano, Gwarzo, Zai Cika Shekaru 65 da Haihuwa

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan JiharKano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, zai…