Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen jihar Kano dake tashar kofar Wambai ta bukaci Gwamnatin jihar Kano da ta samar da kwamatin kar ta kwana da zai rika bibiyar tashoshin motocin da suke daukar fasinjoji ba bisa ka’idaba.

Shugaban Kungiyar tashar motoci ta Kofar Wambai Alh. Salisu Sani Ya:u Gareka ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin Klkungiyar dake tashar Kofar Wambai.

Alh. Salisu Sani yace, daukar fasinjoji a bakin titina na kawowa harkokin sufuri tasgaro wanda hakan yana hana bangaren sufuri habaka kamar sauran jihohi, inda yace, “akwai bukatar Gwamnati ta dauki matakan da za su kawo karshe wannan matsala wadda ta dade tana ciwa masu sana’ar sufuri tuwo a kwarya.”

Shugaban Kungiyar ya kuma jaddada aniyar Kungiyar tashar motoci ta kofar wambai na ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar Kano goyan baya a akodaushe domin Samar da sabbin tsare tsare da abubuwan da za su k ara habaka harkokin sufuri na jihar Kano.

Alh. Salisu Sani yace kamar Yadda jihar Kano ta yi suna a bangaren kasuwanci, za ta yi shura a bangaren harkokin sufuri idon har aka samu sauye sauye musamman ta bangaren bin dokokin da Gwamnati da hukumomin dake lura da fannin sufuri suka sanya da kungiyoyin sufuri.

Salisu Sani ya shawarci direbobin matuka motocin haya na jihar Kano da kasance masu bin dokokin da aka sanya na Shiga cikin tashoshin motoci domin kaucewa zurarewar kudaden Gwamnati Wanda da sune Gwamnatin take samun damar gudanar da ayyukan ci gaba a fadin jihar Kano.

Daga karshe shugaban kungiyar yace, “kngiyar tashar motoci ta kofar wambai a shirye take domin ci gaba da habaka muradun Gwamnatin jihar Kano na tabbatar da ci gaba da samarwa matasa ayyukan yi domin dakile shaye shayen muggwan kwayoyi da kwacen wayoyin alumma da sauran munanan dabi’u.

Haka zalika, yayi Kira ga dukkannin ‘ya’yan Kungiyarsa da su ci gaba da baiwa Kungiyar goyan bayan da suka kamat mm bffa domin ciyar da alummar da Kungiyar matuka motocin haya ta kasa reshen jihar Kano gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Remi Tinubu Ta Shawarci Matasa Su Rungumi Hakuri, Su Guji Dabi’ar Roƙo

Daga:  Abdullahi Bashir  Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci matasan…

Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Majalisar dokokin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta fara…

Al’umar Unguwar Gobirawa Sun Bukaci Dan Majalisa Ya Kammala Musu Hanya

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Al’ummar Gobirawa Sun Bukaci Alhaji Aliyu Sani Madakin Gini…

Za Mu Ci Gaba da Tattara Kudaden Haraji – Shugaban ‘Yan kasuwar Tashar Malam Kato

Daga: Ibrahim Sani Gama KANO – Kungiyar ‘yan kasuwa dake tashar motoci…