Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar tsofaffun daliban makarantar kwalejin Bagauda dake Dakatsalle ta jaddada aniyar na dawo da kwalejin domin bunkasa harkokin ilimi da barwa ‘yan baya damar morar ilimin fasaha musamman a wannan lokacin da muke ciki na nuna fasaha a kasashen duniya.
Shugaban Kungiyar, Injiniya Mustapha Hassan ne ya jaddada hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a nan jihar Kano.
Shugaban kungiyar yace akwai bukatar Gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su baiwa kungiyar tsofaffun daliban makarantar kwalejin Bagauda cikakken hadin kan daya kamata domin ciyar da kwalejin gaba.
Injiniya Mustapha Hassan yace, duk wanda zai kawo gudunmawa komai kankantarsa, Inda kuma yace “duk sanda suka jiyo wani abu da zai taimakawa makarantar suna iya kokarinsu yanda yakamata domin ganin an dawo da kimar wannan makaranta.
Shugaban Kungiyar da cewa, tsofaffun daliban makarantar kwalejin bagauda suna da zumunci a tsakaninsu, musamman a lokacin da Kungiya ta bukaci ganinsu.

Mustafa Hassan yace, ya ga Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ziyarci makarantar kwalejin kuma yace suna da tabbacin cewa Gwamnan zai duk maiyiyuwa wajen tallafawa makarantar.
Shugaban Kungiyar yace, Gwamnati tana iya kokarinta ta yadda ta gyara sauran kwalejin koyar da zana’oin da dalibai zai koyi abubuwa da dama Musamman ilimin fasaha ta Yadda zai yi gogayya da sauran dalibai na kasashen ketare da suka yi fice wajen keraren abubuwa daban daban a zamanance.
Injiniya Mustapha Hassan ya bayyana cewar, kungiyarsa ta san Gwamnatin jihar Kano tana sane da makarantar kwalejin ta bagauda dake dakatsalle kamar yadda ta gyara sauran makarantu tare da Samar da kayayyakin koyo da koyarwa na zamani, musamman yanda kasashen duniya suka shura da yin nisa a bangaren fasahar da dalibi ya koya ba takardar ya samu a matsayin yayi karatu ba.
Haka zalika, shugaban kungiyar yayi kira ga Gwamnatin jihar Kano da ta tuna da makarantar kwalejin bagauda dake dakatsalle kasancewar an rufeta ne sakamakon rashin tsaro wanda yanzu kuma an samu cikakken tsaro a cikin lungu da sako na jihar Kano da ma wajen jihar.
Daga karshe, shugaban kungiyar yace ya san tsofaffin daliban makarantar kwalejin ta Bagauda suna da zumunci da cikakken hadin kai wajen aiwatar da abubuwa, amma duk da haka ya kamata su kara ribanya kokarinsu na tallafawa wannan makaranta, wanda Allah subahanahu wata’la ne kawai zai biyasu a lokacin da bashi da abin za zai iya bayarwa, sadakatul jariyar da ya bayar domin Allah.
