Daga: Sani Muhammad 

Kungiyar Masu Karɓar Fansho ta Najeriya ta ce an kafa ta ne domin kare jin daɗi da walwalar ‘yan fansho, da kuma tabbatar da cewa sun samu haƙƙoƙinsu.

Shugaban reshen ƙungiyar na Jihar Kano, Kwamared Shu’aibu Musa Jibril, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da manema labarai a Kano.

Ya ce shugabannin da suka gabata sun bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa da inganta tsarin fansho.

A cewarsa, manufar kafa ƙungiyar ita ce tabbatar da cewa ‘yan fansho sun samu alawus-alawus da sauran haƙƙoƙin da suka cancanta.

Kwamared Shu’aibu ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin ‘yan fansho, tare da tabbatar da biyan kuɗaɗen fansho cikin lokaci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Babban Al’amari: Yarinya Ta Haddace Qur’ani A Makarantar Raudatul Jannah – Mai Sikeli

Daga: Idris Aliyu Ishaq An bayyana ce wa samun ‘yar shekaru 6 da…

Gwamnatin Kano Ta Sulhunta ’Yan Takarar Majalisar Tarayya Na APC

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…

Tambuwal Ya Fice Daga PDP, Ya Shiga ADC

Daga: Garba Hamza Yakasai Tsohon gwamnan jihar Sokoto State kuma Sanata mai…

Matsayar Saudiyya Kan Ranar Ƙaramar Sallah

Daga: Idris Aliyu Ishaq Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa ba…