Daga: Kabir Getso
Mukaddashin Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Unguwar Zoma ta Ƙasa (National Association of Nigeria Nurses and Midwives – NANNM) reshen Jihar Kano, Kwamared Nas Ahmad Shamzad Sharada, ya bayyana mamakinsa kan kalaman da Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi game da ma’aikatan jinya da unguwar zoma.
Kwamared Shamzad ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da aka gudanar a harabar sakatariyar kungiyar da ke Kano, inda ya jaddada cewa ma’aikatan jinya da unguwar zoma na daga cikin ginshiƙan kiwon lafiya da ke jajircewa wajen ceton rayukan al’umma, ta hanyar aiki dare da rana a asibitoci da cibiyoyin lafiya daban-daban.

> “Girma irin na Mataimakin Gwamna bai kamata ya rinka fitar da irin waɗannan kalamai ga ma’aikatan da ke bin doka da tsarin aiki na gwamnati ba,” in ji Kwamared Shamzad.
Ya ƙara da cewa dukkan ma’aikatan gwamnati a Jihar Kano suna aiki tukuru wajen bin dokokin aiki da ka’idojin gwamnati domin cimma nasarar da Gwamnatin Jihar ke muradi. Ya ce musamman ma’aikatan jinya da unguwar zoma sun dade suna taka rawar gani wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya.
“Ma’aikatan jinya da unguwar zoma ne ke aiwatar da kusan kashi 75 cikin ɗari na dukkan ayyukan asibiti,” in ji shi.
A nasa jawabin, Sakataren Kuɗi na kungiyar, Kwamared Yahaya Shehu Muhammad, ya bayyana cewa bai dace irin waɗannan kalamai su fito daga bakin Mataimakin Gwamna ba, kasancewar shi ma mutum ne mai rai da lafiya wanda wata rana ma ka iya zama Gwamna.

> “Don haka, muna roƙon Mai Girma Gwamna da ya duba wannan lamari don ƙarfafa gwiwar ma’aikatan jinya da unguwar zoma wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu,” in ji shi.
Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da ingantaccen kiwon lafiya a jihar, tare da buƙatar gwamnatin Kano ta nuna ƙauna da goyon baya ga ma’aikatanta.
Sai dai duk kokarin da aka yi na jin ta bakin Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamna kan wannan batu, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bai sami nasara ba.
