Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci shugabannin kafafen yaɗa labarai da su riƙa mayar da hankali wajen bincike kan ayyukan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi kamar yadda suke yi wa gwamnatinsa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a daren Juma’a yayin da ya karɓi bakuncin masu mallakar kafafen yaɗa labarai da manyan shugabanninsu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Aso Rock Presidential Villa.

Ya ce gwamnatinsa ta buɗe tsarin tarayya ta yadda ƙananan hukumomi yanzu ke samun kuɗaɗensu kai tsaye, yana mai cewa ya kamata kafafen yaɗa labarai su sa ido kan yadda ake amfani da waɗannan kuɗaɗe.

“Kada ku riƙa matsa min ni kaɗai. Ku duba abin da ƙananan hukumomi da kuma gwamnatocin jihohi ke yi da kuɗaɗen da suke samu,” in ji shi.

Shugaban ya ƙara da cewa rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a gwamnati tana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasar dimokuraɗiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Dillalan Rimin Zakara Sun Kori Annitaja Daga Shugabancinta

Daga: Rayyan Hassan Kungiyar dillalan dake Rimin Zakara a karamar hukumar Ungogo,…

Majalisa Ta Amince Da Kudirin Kafa Sabuwar Hukuma A Kano

  Daga: Muhammad Adamu Abubakar Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da kudirin…

Da Dumi-Dumi: Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci Ya Yi Murabus

Ƙaramin Ministan Ma’aikatar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr. Yusuf Tanko…

Tinubu Ya Amince Da Kashe Naira Biliyan 46 Domin Sake Gina Titin Sauka Da Tashi Jirage Na Malam Aminu Kano

Daga: Abdullahi Bashir Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ware Naira…