Daga: Abdullahi Bashir
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da takwaransa na Rwanda, Paul Kagame, sun sake nuna jajircewarsu wajen karfafa hadin kai da bunkasa alakar diflomasiyya tsakanin kasashensu domin ci gaban Afirka.
Ganawar shugabannin biyu ta gudana ne a Fadar Urugwiro da ke Kigali bayan isar Tinubu kasar Rwanda domin halartar taron shugabannin kamfanonin Afirka.

Shugabannin sun amince da farfado da Kwamitin Hadin Gwiwar Ministoci na Dindindin (JPMC), tare da yanke shawarar cewa Najeriya za ta karbi bakuncin taron kwamitin na gaba domin zurfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
Tinubu ya kuma bayyana cewa Najeriya za ta yi la’akari da bai wa ‘yan Rwanda damar shiga kasar ba tare da biza ta kwanaki 30 ba, a wani mataki na inganta manufar hadin kan Afirka da saukaka zirga-zirga tsakanin kasashen nahiyar.
Haka kuma, shugabannin sun tattauna kan aiwatar da yarjejeniyoyin fahimtar juna da suka shafi yawon bude ido, yaki da miyagun kwayoyi da cin hanci da rashawa, tare da tabbatar da goyon bayansu ga yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta Nahiyar Afirka.

Najeriya na ci gaba da fadada damar kasuwanci a Afirka, yayin da ake tattaunawa da RwandAir domin samar da karin hanyoyin fitar da kayayyakin ‘yan kasuwar Najeriya zuwa sassan nahiyar.