Daga: Saminu Ibrahim Magashi

Masu saye da sayar da filaye a garin Rimin Zakara da ke Kano sun koka kan yadda suke zargin Kwamishinan Ƙasa na Jihar Kano da muzanta su tare da jefa su cikin rigingimu da abokan cinikayyarsu.

Shugaban dillalan filaye na Rimin Zakara, Alhaji Naziru Annatija, ne ya bayyana koken ’yan ƙungiyar, inda ya ce yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da lamarin na jefa dillalan cikin matsaloli tare da haddasa rashin jituwa tsakaninsu da mutanen da suka sayar wa filaye.

A nasa jawabin, wani daga cikin dillalan garin, Ishaq Abba Shawus, ya ce dillalan ba sa samun sukuni sakamakon yadda yake zargin Kwamishinan Ƙasa da ƙoƙarin haddasa rikici tsakaninsu da waɗanda suka sayar wa filaye.

Ya ce, duk da bayanin da Kwamishinan ya yi a gidajen rediyo cewa an biya kuɗin garin Rimin Zakara, dillalan sun bayyana cewa ba a biya su ko sisin kwabo ba, sai dai abin da suka ce ƙoƙari ne na ƙwace filayen al’umma masu ƙaramin ƙarfi.

Shi ma Alhaji Sulaiman Dangadi, shugaban ɓangaren Rijiyar Zaki, ya roƙi Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba lamarin tare da bincikar yadda ake tafiyar da al’amuran ƙasa a Rimin Zakara.

Alhaji Sulaiman ya ce gwamnati ya kamata ta kasance mai sasanta rigingimu tsakanin al’umma, ba wai ta zama sanadin ƙara haifar da su ba.

Haka kuma, wasu daga cikin masu mallakar filaye a Rimin Zakara sun bayyana damuwarsu kan abin da suka ce ƙoƙarin durƙusar da su da ƙwace musu filayensu, inda suka roƙi Gwamnan Kano da ya kawo musu ɗauki tare da tabbatar da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Remi Tinubu Ta Shawarci Matasa Su Rungumi Hakuri, Su Guji Dabi’ar Roƙo

Daga:  Abdullahi Bashir  Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci matasan…

Majalisar Wakilai Ta Fara Bincike Kan Aiwatar Da Manufar CNG Ta Gwamnatin Tarayya

Daga: Tanimu Salihu Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta fara gudanar da bincike…

Za Mu Ci Gaba da Tattara Kudaden Haraji – Shugaban ‘Yan kasuwar Tashar Malam Kato

Daga: Ibrahim Sani Gama KANO – Kungiyar ‘yan kasuwa dake tashar motoci…

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Ya Halarci Jana’izar Hajiya ’Yandalla

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…