Daga: Shehu Suleiman Sharfadi 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya halarci jana’izar marigayiya Hajiya Habiba Garba ‘Yandalla, tsohuwar shugabar mata ta jam’iyyar APC a jihar Kano, tare da iyalai, abokan siyasa da sauran masu jimami.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a ta ofishin mataimakin gwamnan, Na’ima Musa Umar, ta sanyawa hannu kuma ta rabawa manema labarai a Kano.

Marigayiya Hajiya Habiba Garba ‘Yandalla, wadda ta rasu bayan fama da jinya mai tsawo tana da shekaru 53 a duniya, ta kasance daya daga cikin fitattun mata ‘yan siyasa masu aiki a matakin kasa da kasa, wadanda gudummawarsu ta wuce bayyanawa a kafafen yada labarai da tarukan jama’a.

Gudummawar da ta bayar ta ta’allaka ne wajen hada kan jama’a, gina tsarin jam’iyya da kuma nuna cikakken jajircewa a harkokin siyasa. A tsakanin ‘yan jam’iyyar APC a Kano, an san ta da biyayya da sadaukarwa wajen bunkasa shigar mata cikin siyasa da kuma karfafa ayyukan jam’iyya a matakin kasa.

An gudanar da sallar jana’izarta ne a Hotoro Tsamiyar Boka bayan sallar La’asar, kafin daga bisani aka binne ta a makabartar Tarauni da ke Kano.

Alhaji Murtala Sule Garo ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya jikanta da rahama, sannan Ya sanya ta cikin Aljannatul Firdaus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Muna Alfahari Da Dalibanmu A Jami’o’i A Fadin Najeriya — Bashir Danzomo

Daga: Kabir Getso  Shugaban Husaini Adamu Federal Polytechnic Kazaure, Engr. Dr. Bashir Ahmad…

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirin Hada Gwiwa da Kungiyar Injiniyoyi ta Kasa Don Tabbatar da Ingancin Ayyuka

Daga: Ibrahim Sani Gama Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci…

Zamu Karbi Shawarwarin Hukumar Kiyaye Hadurra Domin Dakile Yawaitar Hadurra A Gadar Dakatsalle

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin jihar Kano ta bukaci hukumar kiyaye hadurra…

Taimakawa Masu Karamin Karfi: Ciyaman Caucas Ungogo LG Yayi Kira

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban kwamitin Dattawa na karamar hukumar Ungogo ya nemi…