Daga: Saminu Ibrahim Magashi

Masu saye da sayar da filaye a garin Rimin Zakara da ke Kano sun koka kan yadda suke zargin Kwamishinan Ƙasa na Jihar Kano da muzanta su tare da jefa su cikin rigingimu da abokan cinikayyarsu.

Shugaban dillalan filaye na Rimin Zakara, Alhaji Naziru Annatija, ne ya bayyana koken ’yan ƙungiyar, inda ya ce yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da lamarin na jefa dillalan cikin matsaloli tare da haddasa rashin jituwa tsakaninsu da mutanen da suka sayar wa filaye.

A nasa jawabin, wani daga cikin dillalan garin, Ishaq Abba Shawus, ya ce dillalan ba sa samun sukuni sakamakon yadda yake zargin Kwamishinan Ƙasa da ƙoƙarin haddasa rikici tsakaninsu da waɗanda suka sayar wa filaye.

Ya ce, duk da bayanin da Kwamishinan ya yi a gidajen rediyo cewa an biya kuɗin garin Rimin Zakara, dillalan sun bayyana cewa ba a biya su ko sisin kwabo ba, sai dai abin da suka ce ƙoƙari ne na ƙwace filayen al’umma masu ƙaramin ƙarfi.

Shi ma Alhaji Sulaiman Dangadi, shugaban ɓangaren Rijiyar Zaki, ya roƙi Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ya duba lamarin tare da bincikar yadda ake tafiyar da al’amuran ƙasa a Rimin Zakara.

Alhaji Sulaiman ya ce gwamnati ya kamata ta kasance mai sasanta rigingimu tsakanin al’umma, ba wai ta zama sanadin ƙara haifar da su ba.

Haka kuma, wasu daga cikin masu mallakar filaye a Rimin Zakara sun bayyana damuwarsu kan abin da suka ce ƙoƙarin durƙusar da su da ƙwace musu filayensu, inda suka roƙi Gwamnan Kano da ya kawo musu ɗauki tare da tabbatar da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Jami’an Gwamnati Daga Bangarori Daban-Daban Na Kawo Ziyarar Ta’aziyya Gwamnatin Kano

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da…

JIBWIS Ta Yaba Wa Gwamnatin Kano Kan Rabon Kujerun Hajji

Daga: Abdullahi Bashir Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya karɓi shugabannin Ƙungiyar Jama’atu…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Alƙawarin Samar da Kayayyakin Koyo da Koyarwa a Manyan Makarantu

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na…

Zulum Ya Ware N12.9bn Don Daukar Nauyin Dalibai 54 ’Yan Borno A Fannin Jiragen Sama Da Injiniyoyi

Daga: Kabir Getso Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da…