Daga; Abdullahi Bashir

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sake lashe zaben gwamnan jihar, inda ya samu nasarar komawa kan kujerar na wa’adin karo na biyu.

Adeleke, dan takarar jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, yayin da babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, ya samu kuri’u 444,815.

Dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Najeem Salaam, ya zo na uku da kuri’u 17,180.

Jami’in zaben na INEC, Farfesa Joshua Ogunwole, ne ya bayyana sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Osogbo, babban birnin jihar, a safiyar yau Lahadi.

Adeleke ya samu nasara a kananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar, yayin da Oyebamiji na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11.

Wannan nasara ta bai wa Adeleke damar ci gaba da jagorantar Jihar Osun na karin wa’adin shekaru hudu a karo na biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Guguwar Sauyin Sheƙa: Peter Obi Da Manyan ADC Na Shirin Ficewa Zuwa Sabuwar Jam’iyya

Daga: Abdullahi Bashir Wasu manyan shugabannin jam’iyyar ADC, ciki har da tsohon…

Dalilin Da Ya Sa Atiku Bai Halarci Taron G-100 Ba — ADC

Daga: Abdullahi Bashir Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana dalilin da…

Kungiyar Jinya da Unguwarzoma: Gwamna Zulum Ya Daga Darajar Ma’aikatan Lafiya a Borno

Daga: Kabir Getso Shugaban kungiyar ma’aikatan jinya da unguwarzoma ta kasa, reshen Jihar…

SABATURE FOUNDATION: Ta Bada Tallafi Ga Makarantar Alkausara, A HDawakin Tofa

Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa A kokarinta na kara bunkasa harkokin ilimi,…