Daga Hamza Yakasai
Akalla mutane 160 ne suka jikkata, wasu daga cikinsu cikin mawuyacin hali, sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai a wasu garuruwa biyu da ke kudancin Isra’ila kusa da cibiyar binciken nukiliya.
Hukumomin agajin gaggawa sun ce mutane 84 sun jikkata a garin Arad, yayin da wasu 78 suka samu raunuka a Dimona, bayan harin makamai masu linzami masu ƙarfi da aka kai a yammacin jiya Asabar.

Sai dai wata Hukumar Kula da Makaman Nukiliya ta Duniya (International Atomic Energy Agency (IAEA) ta ce ba ta da masaniya kan wata barna da ta shafi cibiyar binciken nukiliya da ke kimanin kilomita 13 daga garin na Dimona.
A baya, kafar talabijin ta gwamnatin Iran ta bayyana cewa harin na mayar da martani ne ga wani hari da aka kai kan cibiyar nukiliyar Natanz a ranar Asabar.
A ranar Lahadi kuma, aƙalla mutane bakwai sun jikkata sakamakon wani sabon hari da aka kai kan Tel Aviv, a cewar jami’an agajin gaggawa.
Rundunar sojin saman Isra’ila ta ce Tehran ta harba makamai masu linzami 400 tun bayan harin haɗin gwiwa na Amurka da Isra’ila a ranar 28 ga Fabrairu, inda ta ce kashi 92 cikin 100 an dakile su.

Mazauna Arad sun bayyana cewa karar fashewar da suka ji na da matuƙar firgitarwa, yayin da hare-haren suka lalata gine-gine da dama tare da haifar da babban rami.
Wata jami’ar lafiya, Naram Zaid, ta shaida wa kafarki yada labarai ta BBC cewa ta ga yara da dama da suka samu raunuka a kai da kirji sakamakon faɗuwar abubuwa a cikin gine-ginen da suka lalace.
Ta ce ta taimaka wa wata yarinya mai shekara 10 da ta ji rauni a kai, wadda ta ƙi shiga motar asibiti har sai da aka ceto iyayenta daga ginin da ya rushe, kafin daga bisani a kai su asibiti.
Shugaban ƙasar Benjamin Netanyahu da kuma shugaban ƙasa Isaac Herzog sun ziyarci wuraren da lamarin ya shafa a yau dinnan.
Ana ci gaba da bincike domin gano yadda makaman suka iya tsallake tsarin kariyar sararin samaniyar Isra’ila, lamarin da ke sake nuna illar da yaƙin ke haifarwa ga rayukan fararen hula.