Daga: Mukhtar Yahaya Shehu 

Dalibai Maza Da Mata Dari Da Sittin Da Uku (163) Ne Suka yi Saukar Alqur’ani A Makarantar ABDULLAHI BIN MAS’UD Kuntau da ke Dorayi babba a Karamar hukumar Gwale inda Dalibai 43 Suka Haddace Alku’ani.

A jawabinsa Shugaban Makarantar Malam Aminu Hassan Ya bayyana irin Nasarorin Da Makarantar take Samu a Tsawon Shekaru 14 da aka Kafa ta,Inda yace hakan ya Samu ne Saboda Goyon bayan Mutanen Yankin Musamman Iyayen Yaran . Shugaban makarantar.

ya Kara da godiya ga Wasu Manyan Daidai kun Jama’a da ya ce Basa son a bayyana Sunayen su kasancewar Kullum Suna bayar da gudunmawa ta Kowanne bangare Idan bukatar hakan ta taso.

Ana sa Jawabin babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kano akan harkar Addinai Mal Ali Bichi Wanda ya Wakilci Gwamnan Jihar Kano EngrAbba Kabir Yusif ya bayyana Muhimmamcin koyaw da Ilmi Musamman na Alqur’ani ga yara Matasa a Wannan Lokacin. Inda Yace Shi ne Zai Bude Musu Tunani da zai Basu Hasken Fahimtar Rayuwar Su A Duniya Da Lahira.

Shima Malami Mai jawabi Farfesa Umar Sani Fagge ya Fadakar da dalibai da Mahalarta taron Fa’idar Koyon Alqur’ani da yadda Yawaitar Masu Ilmin sa Suke Jawo Yalwar Arziqi A Cikin Al’Umma.

Ya Kuma ce kiyar da Ilmin Alqur’ani yana Kara Kusanta Mutane da tsoron Allah da Sanin Iyakokin Sa a Kowanne Lokaci

Shi Kuwa Babban Bako Alh Idris Sanusi Bayero (Sarkin Sullubawa) Hakimin Sumaila ya bukaci Iyaye da su Kara sanya idanu wajilen tura yaransu makaranta domin Samun Ilmin Alqur’ani, Inda ya ce wannan Shi ne tushen Gina rayuwar duk Wani Mahaluki Kuma Sh ine Garkuwa Ga Kowanne Musulmi.

Alhaji Idris Bayero ya hori Iyaye da su kara kokari wajen cigaba da tallafa wa Makarantun Addini domin Koyar Da Yara Shi ne Zai bawa Masu Daukar Nauyin Makarantun da Malamai Damar Samun bawa yaran Nagartaccen Ilmi.

Ya Kuma yaba wa Shugabancin Makarantar ta ABDULLAHI BIN MAS’UD Bisa Kokari da Suke wajen bada Tarbiyya ga yara da ke Yankin tsawon Shekaru sama da Goma.

Bayan Karbar Alluna ga Daliban da Suka yi Saukar an Biya Musu Darasu Wanda Ya Nuna Kammala Karatun Saukar Ta Alku’ani.

Bikin Ya Sami Halartar Manyan Mutane da Suka hada da Malamai Da Masu Sarautar Gargajiya da Iyayen yara da Sauran Al’Ummar Musulmi da ke Fadin Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Hukumar DMCSA Ta Yi Bikin Cika Shekaru Uku a Karkashin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf

Daga: Kabir Getso ‎ ‎Taken Bikin ya mayar da hankali kan bayyana wani…

Kwamitin Lafiya Na Masarautar Karaye Ya Ziyarci Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Kwamitin lafiya na Masarautar Karaye karkashin jagorancin Matawallen…

Zamu Baiwa Gwamnatin Jihar Kano Baya Domin Samarwa Matasa Sana’o’in Dogaro Kai

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar matasan yankasuwa dake kasuwar Singa ta bayyana…

Shekarau Gains Tinubu Support Groups’ Backing After Gov. Abba’s Endorsement

By: Mukhtar Yahaya Shehu  The Tinubu Support Groups under the leadership of Dr.…