Daga: Ibrahim Sani Gama

Mutane 176 da aka sace a hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai kauyukan Woro da Nuku da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara a ranar 3 ga Fabrairun shekarar nan, sun samu ‘yanci bayan sun shafe kusan wata shida a hannun masu garkuwa da su.

Gwamnatin Jihar Kwara ta tabbatar da sakin mutanen, inda ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan rawar da suka taka wajen ganin an kubutar da su.

Yawancin wadanda aka sace mata da kananan yara ne. Sun shiga hannun ‘yan ta’addar ne bayan mamayar da aka kai wa kauyukan na Woro da Nuku, inda aka kashe mutane da dama tare da kona gidaje.

Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, ba a bayyana yadda aka samu sakin mutanen ba, kuma ba a tabbatar ko an biya kudin fansa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Sakon Karrama Jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, A Lokacin Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya A cikin wani sakon karramawa da aka gabatar…

ADC Ta Shawarci Al’ummar Kano Da Kasa Su Mara Mata Baya Don Inganta Rayuwa

By: Kabir Getso Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a jihar…

Murtala Garo Ya Yabawa Hafiz Abubakar, Ya Nemi Shawarwari Domin Cigaban Kano

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…

Yin Shugabanci Nagari Da Gudanar Da Ayyuka Masu Ma’ana – Gawuna

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Gawuna ya karɓi ragamar shugabancin hukumar gudanarwar bankin…