Daga: Abdullahi Muhammad

Abuja — Gwamnatin Tarayya ta amince da karin kudin jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO, inda ta kayyade sabon kudin zuwa N50,000 ga kowane ɗalibi, wanda zai fara aiki daga shekarar 2027.

Sanarwar ta fito ne daga Daraktan Sashen Ilimin Manyan Makarantun Sakandare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Adeniji Ibrahim, wanda ya ce matakin ya biyo bayan bukatar da Hukumar Shirya Jarabawar Kasashen Yammacin Afirka (WAEC) ta gabatar na neman a sake duba kudin jarabawar Senior School Certificate Examination (SSCE) da za a gudanar daga shekarar 2027.

A cewar sanarwar, sabon tsarin kudin zai shafi jarabawar WAEC da NECO ga ɗaliban makarantun sakandare a fadin Najeriya, domin samar da daidaito a kudaden da ake karba.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske kan ko Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa wasu rukunan ɗalibai wajen biyan kudin jarabawar ba, ko kuma dalilan da suka sa aka amince da karin kudin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Ya Kamata Gwamnati Ta Sanya Kungiyar Jami’an Sintiri Acikin Tsarin Samar Da Tsaro Tun Daga Jiha Har Tarayyar Kasa

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar jami’an tsaro da kula da gandun daji…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Yin Aiki Da Kungiyar ‘Yan Jaridu Domin Tallata Manufofinta

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na yin…

Hukumar Kula da Hanyoyi da Zirga-zirga ta Jihar Kano (KAROTA) ta fara aikin tantance ma’aikatanta domin gano ma’aikatan bogi a cikin jami’anta

Hukumar Kula da Hanyoyi da Zirga-zirga ta Jihar Kano (KAROTA) ta fara…

‎Al’ummar Jihar Borno Zasu Dade Suna Tuna Gwamna Zulum Bayan Wa’adinsa – ‎Hon Bundi

Daga: Kabir Getso Babban Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Borno Akan Kafafen Yaɗa…