Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na yin aiki kafada da kafada da kungiyar ‘yan jaridu ta kasa domin tallata manufofin gwamnatin jihar.
Mataimakin gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne a madadin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya furta hakan yayin da kungiyar ‘yan jaridar ta kasa karkashin jagorancin shugabanta Kwamared Alhassan Yahaya suka kawo masa ziyarar ban girma a ofishin sa dake gidan gwamnati.
Kwamared Gwarzo ya bayyana cewar, kungiyar yan jaridu ta kasa na daya daga cikin kungiyoyin kwararru dake da karfi kuma dadaddiyar kungiya a fadin kasarnan.
Mataimakin gwamnan ya kuma nuna farin cikinsa bisa wannan wakilci da yayi na gwamnan jihar a Abuja a yayin da kungiyar ke murnar bikin cikarta shekaru 75 da kafuwa.

Ya kuma bayyana cewar idan kana magana akan kungiyar yan jaridu ta kasa kana magana ne a kan siyasar kasarnan,tattalin arzikinta da zamantakewarta kuma kana magana ne akan wani jigo dake da kyakkyawar manufa wajen gina cigaban alummar kasarnan.
Kazalika kwamared ya kuma yaba musu bisa wannan ziyarar da suka kawo jihar tare kuma da zabar jihar kano domin gudanar da taron majalisar zartarwa na kungiyar.
Shima anasa bangaren kwamishinan yada labarai da kuma harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana jin dadinsa dangane da yadda kungiyar ta karrama gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan al’umma kuma abokin kowa watanni biyu da suka gabata.
Ya kuma yaba musu bisa zabar jihar Kano a matsayin jihar da zasu gudanar da taron majalisar zartarwa na kungiyar.
Shima anasa bangaren, shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa Kwamared Alhassan Yahaya ya bayyana cewar sun zabi jihar kano ne domin kungiyar ta nuna wa ‘ya’yanta irin ayyukan cigaba da gwamna Alhaji Abba kabir Yusuf ya gudanar da kuma wadanda ake gudanar wa a fadin jihar.
Shugaban, ya kuma yaba wa gwamnatin jihar bisa yanda take aiki kafada da kafada da ‘yan jaridu da kuma kulawa da walwalarsu, inda ya bada tabbacin gamsuwar su da irin gagarumin ayyukan cigaba da suke gudana a fadin jihar.
Daga karshe, akilinmu na ofishin Mataimakin Gwamna ya ruwaito swear, taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da ‘yan jaridu daga sassa daban-daban na fadin kasarnan.