Daga: Abdullahi Bashir

Jami’an tsaro a birnin Baghdaza sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga da suka taru a yankin gwamnati bayan barkewar rikicin yaki tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.

Rahotanni sun ce magoya bayan jam’iyyun Shi’a da dama sun hallara a yankin gwamnati a ranar Litinin, inda kuma ofishin jakadancin Amurka yake, kamar yadda shaidu suka bayyana.

An ce jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin watse da taron. A wasu bidiyoyi da suka yadu, ana kuma jin karar harbe-harbe a wurin.

Tun a daren Lahadi, daruruwan masu zanga-zanga sun taru a abin da ake kira Green Zone, inda ake zargin sun yi yunkurin kutsa kai zuwa ofishin jakadancin Amurka.

A lokacin, jami’an tsaro sun yi amfani da harsasai na gaske, hayaki mai sa hawaye da kuma motar feshin ruwa domin tarwatsa taron.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka da Isra’ila sun kaddamar da wani babban hari kan Iran a ranar Asabar, lamarin da ya haddasa karin tashin hankali a yankin, yayin da Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami zuwa sansanonin Amurka a wasu kasashen yankin Gulf.

Iran na da gagarumar tasiri a fannin siyasa da kuma soja a kasar Iraki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kwalejin Audu Bako Ta Karyata Zargin Kin Bin Umarnin Gwamnatin Jihar Kano

Daga: Kabiru Getso Shugaban Kwalejin koyar da aikin gona ta Audu Bako da…
 

Kungiyar Laburare Ta Kasa Ta Kai Ziyara Gidan Gyaran Hali

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa   Kungiyar Nigerian Library Association (NLA) Kano Chapter takai…

Wata Gidauniya Ta Nemi Haɗin Gwiwa Da Ma’aikatar Jin Ƙai Domin Ciyarwar Watan Ramadan

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Gidauniyar Save Yateem Orphans ta bayyana aniyarta ta yin…