Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana haɗin gwiwar da ke tsakanin Gwamnatin Jihar da Babban Bankin Raya Musulunci (IsDB) a matsayin ginshiƙi wajen aiwatar da tsare-tsaren ci gaban gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Mataimakin Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a madadin Gwamna Yusuf, yayin da ya karɓi mataimakin shugaban bankin mai kula da harkokin gudanarwa, Dr. Rami Ahmad, wanda ya kai ziyarar ban girma fadar gwamnatin jihar Kano.

A cewar Gwarzo, haɗin gwiwar da ke tsakanin Gwamnatin Kano da IsDB zai hanzarta ci gaban ɗorewa a fannoni masu muhimmanci, ciki har da hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi da kuma bunƙasa ƙauyuka.

Ya yaba da irin ayyukan taimako na bankin a sassa daban-daban na duniya, inda ya ce ayyukansu suna inganta rayuwar mutane, kuma Najeriya ba ta keɓanta ba, musamman jihar Kano da ta kasance cikin manyan masu cin moriya.

 

Mataimakin Gwamnan, yayin da yake haskaka muhimman abubuwan da gwamnatin jihar ta mayar da hankali a kai, ya jaddada cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da jagorantar shirye-shiryen da suke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.

 

Haka kuma ya jaddada muhimmancin ayyukan Shirin Raya Noma da Kiwo na Kano (KSADP), inda ya bayyana cewa tsoma bakin shirin a cibiyoyin tara madara, wuraren yanka, hanyoyi da sauran ayyuka suna taka muhimmiyar rawa wajen inganta manufar ci gaban jihar.

 

A nasa jawabin, Dr. Rami Ahmad ya yaba wa jihar Kano bisa jajircewarta wajen tafiyar da mulki mai mayar da hankali kan bukatun al’umma, tare da tabbatar da cewa bankin zai ci gaba da faɗaɗa haɗin gwiwa da jihar.

“Kano ta kasance abokin haɗin gwiwa na musamman ga Babban Bankin Raya Musulunci a Najeriya. Mun gamsu da hangen nesa na gwamnatin, kuma mun kuduri aniyar tallafawa ayyukan da za su bar tasiri mai ɗorewa ga al’umma,” in ji Dr. Ahmad.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Jihar Lagos ta Fara yin Gwajin lafiya ga Maniyyata aikin hajjin bana na Shekara 2026

Gwamnatin Jihar Lagos ta Fara yin Gwajin lafiya ga Maniyyata aikin hajjin…

Tsohon Gwamna Ya Kayar Da Mutane 5 A Neman Tikitin Takarar Gwamnan Bauchi

Daga: Abdullahi Bashir  Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Barrista Mohammed Abdullahi Abubakar, SAN,…

Gwamnatin Jihar Nan Ta Jajantawa ‘Yan Kasuwar Farm Centre Bisa Ibtila’in Gobara

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi A martanin da mai girma mataimakin gwamnan jihar…

Ma’aikatar Jinkai ta Kano Ta Raba Tallafin Abinci Ga Jama’a, Tare da Kai Ziyara Ga Masu Bukata Ta Musamman

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa A ci gaba da kokarinta na rage wa…