Daga: Ibrahim Sani Gama

An yi kira ga Gwamnatin jihar Kano, Karamar hukumar Wudil da ‘Yan majalisar wakilai na jiha da Tarayya, da su kawowa al’ummar mazabar Lajawa daukin gaggawa domin gyara musu hanyar da ta tashi daga ‘Yan Audu zuwa garin Lajawa duba da lalacewar da hanyar tayi.

Shugaban kungiyar matasan yankin Mahamud Nuhu Lajawa ne yayi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a nan jihar Kano.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewar, sun dade suna ta yin kiraye-kiraye ga mahukunta da su zo domin gyara musu hanyar saboda barazanar da suke fuskanta dangane da titin, amma har yanzu ba’a gyara ba.

Yace kungiyar matasan yankin ta taka gagarumar gudunmawa wajen ganin mahukunta sun kawo musu dauki wanda, ya ce kamar yadda suka janyo hankulan al’ummar yankunan suka zabi Gwamnatin to kamata yayi su ma a share musu hawayensu.

Shugaban ya bayyana cewar, har kunyar Alummar yankunansa yake saboda tabbacin da suka baiwa jama’a a yayin da Gwamnati karkashin jagorancin Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf suka yi.

Mahamud Nuhu Lajawa ya kara da cewa, yanzu lokaci yayi da za’a ramawa kura aniyarta na gagin an gyara wannan titi da ya zama kalubale ga al’ummar karamar hukumar Wudil.

Yace, yanzu haka al’ummar yankunan sun fara cewa, idan Gwamnatin ba ta gyara musu hanyar ba, ba za su kara zabar duk wani Dantakara ba tun da basa morar komai daga Gwamnatin da suka zaba ba.

Dan haka shugaban kungiyar matasan yankin yake kiraye-kirayen masu ruwa da tsaki su taimakawa wadannan al’umma domin ganin an samar da wani sabon titin da zai kwantarwa da al’ummar yankunan hankalu.

Mahamud Lajawa ya kara da cewa, mazabar sun kai mutane dubu goma sha biyu wadanda suke da kada kuri”ar da za su zubawa Gwamnatin a kakar zabe mai zuwa, inda yace basa so Gwamnatin jihar Kano mai ci ta rasa wannan kuri’u shi yasa kungiyar matasan yankin take ta yin kiran Gwamnati ta zo domin gyara wannan hanya.

Haka zalika shugaban kungiyar yace, ba za su fasa yin kiraye kirayen mahukunta su zo domin gyara wannan hanya, wanda yace sakamakon gudunmawar da suka bayar yakamata a rama alkhairi da alkhairi, musamman duba da yadda zabe yake karatowa.

Daga karshe Shugaban yayi kira ga al’ummar yankunan da su kara kwantar da hankulansu domin kungiyar matasan ba za ta gajiya ba wajen kiran Gwamnatin a halin da al’ummar suka samu kansu a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Zamu Kashe Sama da Naira Miliyan 87 Dan Sanya Interlock a Sakatariyar Karamar Hukumar Dala Da Kuma Wasu Gyare Gyare a Cikin Karamar Hukumar

Daga: Sani Idris Maiwaya Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe sama…

EFCC Ta Dakatar Da Asusun Gwamnatin Jihar Osun Kwanaki 10 Kafin Zabe

Daga: Abdullahi Bashir Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa…

Nuna Alhini Kan Rasuwar ‘Yan Wasan Kano 21 A Gasar Wasanni Ta Kasa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Bayero Kano kuma Shugaban…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kafa Kwamitin Kafa Kwalejin Fasaha Ta Gaya

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani kwamiti…