Daga: Mas’ud Mato Garo
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a taron Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewacin Najeriya da aka gudanar a Kaduna.
A yayin taron, ƙungiyar ta ƙaddamar da sakatariyarta ta wucin gadi bayan kafata, lamarin da shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana a matsayin tarihi, yana mai ƙara cewa wannan shi ne karon farko da aka samar da sakatariya tun kafa ƙungiyar fiye da shekaru 50 da suka gabata.

Alhaji Murtala Sule Garo ya zauna tare da sauran gwamnoni a wajen taron da aka gudanar a Banquet Hall na Sir Kashim Ibrahim House tsakanin Labara 8 da Alhamis 9 ga Yulin shekarar 2026.
Taron ya mayar da hankali kan batutuwan tsaro, haɗin kai tsakanin jihohin Arewa da kuma hanyoyin bunƙasa tattalin arzikin yankin domin fuskantar ƙalubalen da ke addabar al’umma.
A zaman yini biyun da ya yi a Kaduna, Mataimakin Gwamnan ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouq Ibrahim, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Da shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe yake jawabi, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya yabawa gwamnonin Arewa kan haɗin kan da suka nuna wajen kafa sakatariyar, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa ƙoƙarin warware matsalolin tsaro da ci gaban yankin.
Ya kuma bayyana cewa taron haɗin gwiwa da aka yi tsakanin gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya, tare da kafa kwamitin amintattu na fitattun mutane kan harkokin tsaro, alama ce ta ƙudirin shugabannin yankin na kawo ƙarshen matsalolin satar mutane, ta’addanci da sauran barazanar tsaro.
A madadin gwamnonin Arewa, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yabawa shugabancin ƙungiyar kan wannan mataki tare da jaddada cikakken goyon bayansu domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.