
Daga: Zakariyya Adam Jigirya
A ranar Asabar, 18 ga Oktoba, 2025, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, Ph.D, ya kaddamar da sababbin gine-gine guda biyar (5) da suka ƙunshi azuzuwa goma (10), ofishin malamai da kujerun zama, domin inganta yanayin koyarwa a Makarantar GISS K/Maiyaki, da ke cikin karamar hukumar Kiru, Jihar Kano.
Wannan aiki, wanda ya kasance wani ɓangare na shirin dan majalisar na ci gaban ilimi a mazabarsa, ya sami halartar manyan baki daga hukumomi daban-daban. Cikin wadanda suka halarci bikin akwai Babban Darakta daga Ma’aikatar Upper Niger Development Authority, Mista Joshua Hassan, da kuma dan kwangilar da ya aiwatar da aikin, Alhaji Sani ’Yar Adua, tare da wakilan P.T.A/SBMC, shugaban makarantar da mai taimaka wa dan majalisar (SA), Ashiru Pilot.
A yayin taron, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa ginin zai taimaka wajen rage cunkoson dalibai a ajujuwa da inganta yanayin karatu da koyarwa. Ya kara da cewa, “babu ci gaban al’umma face idan aka inganta ilimi, saboda haka zamu ci gaba da zuba jari a fannin ilimi domin gina kyakkyawar makoma ga ‘ya’yanmu.”

Masu halarta sun yaba da wannan kokari na dan majalisar, suna bayyana shi a matsayin abin koyi ga sauran wakilai, musamman wajen mayar da hankali kan ci gaban ilimi a yankunansu.
A karshe, an gudanar da addu’o’i na godiya da fatan alheri ga dan majalisar, tare da fatan Allah Ya saka masa da alheri ya kuma ba shi ikon ci gaba da irin wannan kokari mai albarka.
