Daga: Ibrahim Sani Gama


Kungiyar ‘yan kasuwa ta Kofar Wambai ta bukaci al’ummar kasuwar da su baiwa Gwamnatin jihar Kano goyan bayan da ya kamata domin samun damar basu tallafin da za su inganta kasuwancinsu yadda ya kamata.

Shugaban kungiyar kasuwar Alh. Jamilu Yahaya Ibrahim ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da kiraye-kirayen da kananan ‘yan kasuwa suke yi domin meman tallafin gwamnati akan sana’o’insu.

Yace, ‘yan kasuwa suna da bukatar tallafin kudade da za su habaka jarinsu domin su zamto masu dogaro da kawunansu har ma su taimakawa wasu.

Shugaban ya bayyana cewar, ya kamata gwamnati ta nemi kungiyoyi na kasuwanni wajen zakulo mutanen da suka cancanci amfana da tallafin da gwamnati ke bayarwa a matsayin ba da jarin sana’o’in da za su samu damar tsayawa da kafafunsu.

Alhaji Jamilu ya kara da cewar, a yanzu ‘yan kasuwa suna Cikin damuwa sakamakon karancin jarin da su rika sana’arsu kamar yadda wasu jihohi da kasashen ketare suka yi domin kara bunkasa tattalin arzikin jihar Kano da ma kasa baki daya.

Alh Jamilu ya jaddada cewar, baiwa matasa da kananan ‘yan kasuwa zai taimaka gaya wajen habaka tattalin arzikin jihar Kano da rage masu rashin ayyukan yi da rage yawan fadace-fadacen daba cikin birnin Kano baki daya.

Ya bayyana cewar, kungiyar kasuwar Kofar Wambai a shirye take wajen ganin ta marawa gwamnatin jiha baya a duk wasu tsare-tsare da ta zo da su domin inganta rayuwar al’ummar Kano.

Haka zalika, ma’aikatar kasuwanci ta jihar Kano da ta yi duba na tsanaki tare da tunawa da kananan ‘yan kasuwa ta hanyar basu horo akan kasuwancinsu da basu tallafin jari na musamman a harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

Daga karshe yayi kira ga kananan ‘yan kasuwa da su mayar da hankalinsu wajen alkinta duk wani tallafin da gwamnati za ta bayar da sanyasu a cikin kasuwanci domin gwamnatin jihar Kano tana jin kiraye-kirayen da aka yi mata domin neman wata bukata.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Za Mu Ci Gaba da Tattara Kudaden Haraji – Shugaban ‘Yan kasuwar Tashar Malam Kato

Daga: Ibrahim Sani Gama KANO – Kungiyar ‘yan kasuwa dake tashar motoci…

Kamfanin Olam Agric ya koyawa mata 355 yadda ake sarrafa fulawa a Kano

Gwamanatin jihar Kano ta yabawa Kamfanin Olam Agric bisa horar da mata…

Mun Shirya Don Baiwa Gwamnati Hadin Kan Sana’ar Magungunan Dabbobi – Kwamared Abdulrahman

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar ‘yan kasuwa masu saida magungunan dabbobi ta kasa…